✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A yi takatsantsan kar a kai wa Siriya hari

A kwanakin da suka gabata ana ta tuntubar juna a tsakanin manyan kasashen duniya, wadanda suka hada da  Amurka da Birtaniya da Faransa, kan yiwuwar…

A kwanakin da suka gabata ana ta tuntubar juna a tsakanin manyan kasashen duniya, wadanda suka hada da  Amurka da Birtaniya da Faransa, kan yiwuwar kai wa shugaban kasar Siriya, Bashar al-Assad hari. Wannan takaddama ta biyo bayan binciken da Majalisar dinkin Duniya ta udanar a kasar kan amfani da makamai masu guba da ake zargin sojojin gwamnati sun yi. Wannan al’amari dai masu lura da al’amura na ganin wata dabara c eta Turawan Yamma da za su fake da ita, don daukar matakin soja a kan gwamnatin Al-Assad.
Hukumar Tsaro ta Majalisar dinkin Duntiya ta kasa yin katabus tun sa’adda aka fara yi wa gwamnatin Assad tarzoma a shekarar 2011. Wannan rikici da ya haifar da zubar da jinin a Siriya ya haifar da takaddama kan hare-haren da sassan da ba su ga maciji ke kai wa juna. An kiyasta cewa kimanin mutum dubu 100 suka rasa rayukansu, kuma fiye da mutum miliyan biyu ne suka zama ’yan gudun hijira. A kwanakin da suka gabata an samu karuwar yawan mata da kananan yara da ke ketara kan iyakar Siriya, don su guje wa yaki.
Matsayan da kasashen Yammacin Turai suka dauka na dora alhakin amfani da makamai masu guba kan sojojin gwamnati tun kafin jami’an bincike su mika rahotonsu, ba adalci ba ne. Manufar kawai a tabbatar da laifi kan gwamnatin Al-Assad kafin bincike. Babu aiki da hankali a ce wata gwamnati a kowace kasa ta kai wa al’ummarta hari da makamai masu guba. Farfagandar kafafen yada labaran da kasashen Turai ke yi wa Siriya makirci ne kawai, don kada hujjar kai harin soja a kan kasar. Zargin da ake yi na cewa Siriya ta yi amfani da makamai masu guba, yaudara ce, tamkar yadda aka yi karyar samun makaman kare dangi, al’amarin da aka fake da shi wajen yakar Gwamnatin Saddam Husseini. Irin wannan yaudarar aka yi amfani da ita wajen yaudarar kasar Sin cewa yakin da ake yi a Libya na ceton al’umma ne, alhali manufar kawai a kawar da gwamnatin kasar. Tun bayan da aka kawo karshen yake-yaken Iraki da Libya, bayan an kashe shugabanninsu da dubbn mutane, wadannan kasashe biyu ba su zauna lafiya ba. Ruruta wutar kai wa Siriya harin da kasashen Yammacin Turai ke yi ba tare da goyon bayan Majalisar dinkin Duniya ba, wannan na nuni da manufar son ran kasashen na rusa rayuka da kaddarori kamar yadda suka taba kwatar a yake-yaken baya.
Baya ga Majalisar Birtaniya da ta ki amince wa Firayiminista Dabid Cameron na kai wa Shugaba Al-Assad na Siriya hari, Shugaba Barack Obama na Amurka har yanzu bai yanke matsaya ba, abin da yake karara a bayyana shi ne tsahirtawar da Shugaba Obama ya yi, don gudun kada ya sake jefa kasarsa cikin wani yamutsin da za a sha wuyar fita.
Sulhu cikin ruwan sanyi shi zai kawo wa Siriya zaman lafiya. Sai dai kin amincewar da kasashen Turai suka na jawo hankali ’yan tawaye su amince da yarjejeniyar sasanci, hujja ce kwakkwara da ke nuni da manufar Amurka da kawayenta, na kin amfani da dabarun difulomasiyya don kawo karshen rikicin Siriya. Tsawon lokaci da Turai ke ingiza ’yan tawaye, sai kara jajircewa suke tare da kai munanan hare-hare a kan sojojin gwamnati. Babbar matsalar da wadannan kasashen da ke son a fafata yaki za su fuskanta ita ce, ’yan tawayen ba su da tsari, kuma ba su yi wani shiri a kasa ba. Sabanin haka ma, masu tsattsauran ra’ayin Musulunci, wadanda ake zargi da alaka da Alka’ida ke fafata yaki.
Wani karin abin damuwar shi ne harin da za a kai wa Siriya tare da goyon bayan Birtaniya da Faransa da Amurka, zai bakanta wa Rasha da China rai, wadanda daukacinsu sun yi gargadi kan daukar matakin soja a Siriya, inda Mosko ta yi nuni da cewa, daukar irin wannan mataki, zai haifar “da mummunan sakamako,” a wannan yanki.
kasashen da suke hankoron daukar matakin soja a kan Siriya, ya kamata su san cewa, in an yaki Siriya ko an kashe Assad ko an kawar da gwamnatinsa, ba za a iya shawo kan rikicin kasar ba, tamkar dai abin da ya faru a Iraki da Libiya. Don haka muke bayar da shawara kan cewa a yi watsi da shirin kai harin soja a kan Siriya. Duk da haka akwai bukatar a dauki mataki dakatar da yaki a Siriya, ta yadda kasar za ta samu zaman lafiya. Dole ne Majalisar dinkin Duniya ta dage kan dabarun difulomasiya na duniya don warware matsalar da ke tsakanin ’yan tawaye da gwamnati.