Shugaban Kasa Bola Tinubu ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai da ’yan uwan wadanda suka mutu sakamakon nitsewar kwale-kwale a Jihohin Neja da Adamawa.
A cikin makon nan ne mutane da dama suka mutu sanadin kifewar kwale-kwale a Karamar Hukumar Mokwa a Jihar Neja da kauyen Gurin a Fuforen Jihar Adamawa.
- Abin da ya hana matatar man Dangote fara aiki bayan wata 4 da kadadamarwa
- Gwamnatin Gombe ta rushe gidajen Gala 5
A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ta bakin Kakakinsa, Ajuri Ngelele, Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan yawan kifewar kwale-kwalen a fadin Najeriya.
Shugaban ya kuma umarci hukumomin gwamnati daban-daban, ciki har da jami’an tsaro da hukumomin kula da sufurin jiragen ruwa da su hada kai wajen gano musabbabin hadurran da ya ce za a iya kauce musu.
Tinubu ya kuma jaddada cewa zai ci gaba da sa’ido wajen tabbatar da dukkan hukumomin gwamnati sun yi abin da ya dace wajen kiyaye rayukan al’umma.
Ya kuma ba iyalan wadanda lamarin ya shafa tabbacin cewa za su yi aiki tukuru wajen ganin hakan ba ta sake faruwa ba a nan gaba.