✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A yi amfani da fasahar zamani don yaƙar ta’addanci — Ganduje

Ganduje ya ce dole ne yaƙi da ’yan tada ƙayar baya da ’yan fashi da makami su tafi tare da haƙiƙanin lokaci domin samun nasara. 

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da shawarar yin amfani da fasahar zamani wajen yaƙi da ta’addanci da ’yan fashi a Nijeriya.

Shugaban ya bayar da shawarar ne a ranar Larabar da ta gabata a lokacin da ya jagoranci mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na ƙasa a ziyarar jaje ga gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni a kan harin da aka kai wa rundunar sojijin barikin soja da ke Buni Gari.

Ganduje ya ce dole ne yaƙi da ’yan tada ƙayar baya da ’yan fashi da makami su tafi tare da haƙiƙanin lokaci domin samun nasara.

Ya bayyana cewa abin takaici ne irin yadda ’yan tada ƙayar baya da ’yan fashi suke aikata munanan ayyuka a faɗin ƙasar nan.

“A yanzu za a yi amfani da albarkatun da ake da su don maye gurbin irin kayan aikin da aka lalata.”

Da yake jawabi, gwamna Buni ya ce gwamnati a matakai daban-daban na duba yadda ake amfani da fasahar zamani wajen yaƙi da ‘yan ta’adda.

“Mu, a matakin ƙasa da gwamnonin yankin Tafkin Chadi, muna yin nazari sosai kan yadda maƙiya ke amfani da jirage marasa matuƙa aikata ta’assar wadda dole mu haɗa kai da jami’an tsaro don duba matsalar,” in ji Buni.

Ya ba da tabbacin cewa za a tattauna hakan a mataki mafi girma musamman da shugaban ƙasa domin daƙile ayyukan tada ƙayar baya da ’yan bindiga.

“Wannan matsala ce ta ƙasa domin a lokacin da suka kai hari a sansanin soji da kuma ƙwace makamai, ba za a iya sanin inda za a yi amfani da su ba, don haka ya kamata a ɗauki waɗannan hare-hare a matsayin hare-hare ga al’ummar ƙasa baki ɗaya ba wai Jihar Yobe kaɗai ba.”