✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A yayin da farashin mai ya kara tashi

A Talatar makon jiya ce farashin danyen mai ya tashi zuwa kimanin Dala 61 ga kowace ganga a kasuwar mai ta duniya, wanda shi ne…

A Talatar makon jiya ce farashin danyen mai ya tashi zuwa kimanin Dala 61 ga kowace ganga a kasuwar mai ta duniya, wanda shi ne farashi mafi girma tun daga Yulin 2015. Akwai alamun da ke nuni da cewa farashin na iya hauhawa zuwa Dala 70 nan da makonni kadan masu zuwa. Wannan na faruwa ne a sakamakon tsuke kasuwa, a kokarin da kungiyar kasashe Masu Mai Ta Duniya (OPEC) na rage yawan man da membobinta ke hakowa. Wannan tsari zai kai har zuwa watan Maris na badi, sai dai kasashen Saudiyya da Rasha sun bayyana bukatar tsawaita lokacin. Ana sa ran ministocin OPEC za su yi taro a hedikwatar kungiyar da ke birnin bienna, Austria a ranar 30 ga watan nan, domin tattauna yiwuwar kara tsawon lokacin na takaita yawan man.

Wannan a zahiri labari ne mai dadi ga Najeriya, musamman idan ta iya dorewa da samar da ganga miliyan biyu a kullum. Saboda kashi 75 na kudin shiga da kuma kashi 90 na cikin kudaden waje da Najeriya ke samu suna fitowa ne daga danyen mai. Sai dai kada a yi saurin murna, domin kuwa farashin na iya faduwa kasa a kowane lokaci. A can baya a 2014, kudin shiga da kasar nan ke samu na kai wa kimanin Dala biliyan 1.4 a kowane wata, amma a dan karamin lokaci sai farashin ya fadi, kudin da ake samu ya ragu sosai zuwa Dala miliyan 300 zuwa 400 a wata. Wannan ke tabbatar da cewa ba a daukar wa farashin mai alwashi.

Koda an samu karin farashin mai ma, na dan karamin lokaci ne, domin kuwa aikin hako mai da Amurka ke kan yi da kuma tsare-tsarenta na bunkasa kimiyya zai haddasa farashin ya sauko kasa. Don haka babu hikima a gare mu, don ganin farashin mai ya hau, a mike kafa, a ce matsalolinmu sun kawo karshe, don haka batun fadada hanyoyin bunkasa tattalin arziki zuwa wasu abubuwan ya zama wajibi. Dogaro da mai shi kadai raguwar dabara ce, domin kuwa dalili ke nan tattalin arzikinmu ke durkushewa da zarar an samu tangarda da farashin mai a duniya. Abin da ya faru ke nan a 2016, yadda Najeriya ta fada karayar tattali arziki, farashin kayan masarufi ya hauhawa, matsin aljihu ya gallabi al’umma. Ga shi har yau din nan, sakamakon yana haddasa matsala ga rayuwar al’ummar kasa.

Duk da cewa shugabanninmu na bayanin cewa za su fadada hanyoyin samun kudin shiga fiye da mai amma an kasa daukar kwakkwaran matakin tabbatar da haka har zuwa sai 2015, jim kadan da hawan zuwan mulkin wannan gwamnati. An dan turza a fannin noma, inda baya ga karafafa arzikin manoman, noman ya taimaka sosai yadda Najeriya ta fita daga matsin tattalin arziki da ya same ta.

Ganin yadda farashin mai ke dagawa, akwai yiwuwar gwamnati ta ce za ta yi saku-saku da al’amarin fadada hanyoyin samun kudin shiga. Yin haka, babban kuskure ne, maimakon haka, yanzu ne ma ya kamata a kara himma sosai wajen fadada hanyoyin samun kudin shiga daban-daban fiye da man fetur. Kamata ya yi duk wata rarar kudi da za a samu a sakamakon wannan sabon farashi na mai, to a mika ta kacokan zuwa nemo wasu hanyoyin na daban. Ya dace a maida himma sosai ga harkokin noma da hako ma’adinai. Ya dace kuma gwamnati ta maida hankali ga gine-ginen kayayyakin more rayuwar al’umma.

Wannan ba lokaci ba ne da za a rika kashe kudi ta hanyar almubazzaranci. A ci gaba da toshe kofofin da ke tsiyayar da dukiyar kasa, a rika amsar haraji yadda ya kamata daga dukkan kamfanoni da cibiyoyin da suka wajaba. Maganar Gwamnoni su zura ido ga daunin da suke samu daga Gwamnatin Tarayya domin biyan albashi da sauransu dole ta canza, dole su mike su nemi hanyoyin kudin shiga daga jihohinsu. Ya kamata kuma a duba batun ma’aikata, kamar yadda kungiyar kwadago (NLC) ta bukata. Lallai a duba albashin ma’aikata domin inganta shi, wanda haka zai bunkasa zimmar ayyukansu ga al’ummar kasa.