Fitaccen malamin Addinin Musuluncin nan na Kaduna, Sheik Ahmad Gumi ya ce ’yan bindiga sun koyi garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ne daga Kungiyar Tsagerun Yankin Neja Delta (MEND)
Gumi ya bayyana haka ne a cikin wani shiri a gidan talabijin na AIT ranar Talata.
Malamin ya ce matukar Gwamnatin Tarayya za ta yi wa ’yan tawayen na Neja Delta afuwa, bai ga dalilin da zai sa a gaza yi wa ’yan bindiga makamancin hakan ba, yana mai cewa hakan ne kadai zai iya kawo karshen matsalar.
Ya ce, “Mun kasa yin abinda ya kamata wajen magance wannan matsalar, shi ya sa har yanzu taki ci taki cinyewa.
“Idan muka ce yin afuwa, ba wai muna nufin duk wani mai aikata laifi a kyale shi ya ci gaba da yawo sakaka ba ne.
“Sun koyi garkuwar ne daga MEND, ban ga wani banbanci tsakaninsu ba. Su aka fara sacewa shanu. Su ‘yan MEND man fetur ne shanunsu. Abinda muke gani yanzu ya ma fi kama da tayar da ta’addanci fiye da ayyukan ’yan bindiga.
“Kusan zan iya cewa kaso 10 cikin 100 na makiyayan ne bata-gari, ba wai 90 ba, sun dauki makamai ne domin su kare kansu.
“Su da kansu za su iya magance matsalar ta hanyar fito da bata-gari daga cikinsu,” inji Sheik Gumi.
A kwanakin baya dai, malamin ya shiga har cikin daji domin tattaunawa da ’yan bindigar domin su ajiye makamansu.
Ya kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi wa ’yan bindigar afuwa, lamarin da mutane da dama, ciki har da Gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufa’i suka ki amincewa da shi, yana mai cewa ba su cancanci yafiya ba.