Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote kuma Shugaban Matatar Man Fetur ta Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce an warware takaddamar rashin ba matatar man fetur, inda ya yi alkawarin Matatar Dangote za ta fara sayar da man a cikin watan Agusta mai zuwa.
Attajirin Afirkar ya bayyana haka ne a lokacin da yake zagayawa da manyan ’yan jarida zuwa Kamfanin Takin Zamani na Dangote da babbar matatar wadda ita ce ta biyu a duniya kuma mafi girma dunkulalliya a duniya a yankin kasuwanci na Dangote da ke Legas a ranar Lahadin da ta gabata.
Ya ce an magance matsalar ce a makon jiya bayan Gwamnatin Tarayya ta sanya baki kan lamarin.
Dangote ya kara da cewa Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ma ya bayar da gudunmawa wajen kawo karshen matsalar.
’Yan bindiga sun kashe mutane 4 sun sace 150 a Zamfara
Idan za a iya tunawa a kwanakin baya Mataimakin Shugaban Kamfanin Man Fetur da Gas na Dangote, Mista Devakumar Edwin ya zargi manyan kamfanonin man fetur na kasashen duniya da yin zagon kasa wajen sayar da danyen mai ga matatar.
Ya ce, manufarsu ta yin haka ita ce matatar ta gaza, kuma suna yin haka ne da gayya ta hanyar tsuga kudin danyen man ko su ce babu danyen man.
“A wasu lokuta mukan yi karin Dala shida a kan farashinsa a kasuwar duniya.
“Sun tilasta mana rage abin da muke tacewa tare da shigo da danyen man mai daga waje har zuwa Amurka abin da ke kara tsadar man,” Edwin ya bayyana a makon jiya.
Alhaji Aliko Dangote, ya ce suna fata manyan kamfanonin mai na duniya za su mutunta maslahar da aka samu.
Game da kason Gwamnatin Tarayya a matatar, Alhaji Aliko Dangote ya ce, gwamnatin tana da kashi 7.2 kacal a matatar sakamakon gaza biyan sauran kudin da zai sa ta mallaki kashi 20 cikin 100.
Tabbacin na Dangote na iya kwantar da hankalin ’yan Nijeriya wadanda suke shiga fargabar rashin mai a matatar na iya jawo tashin kudin mai.
Aminiya ta lura wannan ne karo na uku da matatar ke daga ranar fara sayar da man fetur bayan da ta fara sayar da man dizal da man jirgin sama a kwanakin baya.
Alhaji Aliko Dangote, wanda ya yi dogon bayani kan tarihi da gwagwarmayar da ya sha wajen kafa matatar, ya ce ta kama aiki gadan-gadan ne a wannan shekara inda ta fara tace mai irinsu dizal da man jirgi da polypropylene, naphtha, RCO da sauransu.
Ya ce ana sa ran ta rika tace ganga dubu 500 a kullum wato manyan jiragen ruwa 15 a wata guda daga watan Agusta mai zuwa, inda za ta samar da tan dubu 550 zuwa karshen bana kuma ta samar da tan dubu 650 a wata uku na farkon shekarar 2025.
Matatar dai tana da ma’ajiyoyin mai da za su dauki lita biliya hudu da rabi.
Ya ce, “Matatar Dangote za ta iya biyan bukatar Nijeriya har a samu rarar man da za a fitar kasashen waje.”
Ya ce sun kuma gina bututun gas mai tsawon kilomita 200 da hadin gwiwar Kamfanin NGIC.
Kuma suna da wasu ayyuka a bangaren da suka kai kafa biliyan uku a ma’ajiyar tattara gas na kan tudu ya ce aikin zai taimaka wajen rage nauyin da ke kan bututun Escravos–Legas .
Alhaji Aliko Dangote ya ce aikin kafa kamfanin casar shinkafa mai girman tan miliyan daya na Kamfanin Dangote na ci gaba da gudana, kuma za a kaddamar nan da ’yan watanni.
Ya bayar da tabbacin kamfanin taki na Dangote zai koma aiki nan da mako biyu don samar wa manoma yabanya.
Ya ce ana matukar neman takin Kamfanin Dangote a Nijeriya da kasashen Afirka ta Yamma.
Ya ce, an samu karuwar sarrafa takin zamanin da kashi 48 cikin 100 zuwa tan miliyan 1.2 a shekarar 2023, inda hakan ya samar da aiki 1,500 da aiki 5,000 a kaikaice.
Da ya juya kan siminti, Alhaji Aliko Dangote, ya ce kashi 75 cikin 100 na kudin shigar kamfanin a yanzu na fitowa ne daga kasuwancin siminti.
Ya ce yana fata nan gaba kadan kashi 50 na kudin shigar kamfanin zai fito ne daga wajen Nijeriya ciki har da fitar da kaya, kuma kashi 70 zai kasance Dala da Fam ne da sauran manyan kudaden duniya.
Ya ce, simintin kamfanin ne kan gaba a Afirka inda yake samar da tan miliyan 52 duk shekara a kasashe 10. Ya ce, ya koma harkar masana’antu ne daga saye da sayarwa saboda kaunar da yake wa Nijeriya ta kasance mai dogaro da kanta maimakon gina masana’antun kasashen waje tana daxa jawo wa kanta rashin ayyukan yi.