✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A Takaice… 03

John Mikel Obi zai koma Inter Milan Alamu sun nuna shahararren dan kwallon Najeriya da yanzu haka yake buga kwallo a kulob din Chelsea da…

John Mikel Obi zai koma Inter Milan

Alamu sun nuna shahararren dan kwallon Najeriya da yanzu haka yake buga kwallo a kulob din Chelsea da ke Ingila zai canja sheka a karshen kakar wasa ta bana zuwa Italiya don cigaba da buga kwallo a kulob din Inter Milan.
Kamar yadda wadansu jaridu da ake wallafasu a kasar Italiya suka kalato, tuni Kocin Inter Walter Mazzari ya fara yunkurin tuntubar wakilan Mikel Obi a kan yiwuwar dauke dan kwallon daga Ingila.
Sai a shekarar 2017 ake sa ran kwantaragin Mikel Obi zai kare a kulob din Chelsea amma ganin yadda kulob din ya sayo Nemanja Matic a watan Janairun da ya gabata ta sa Mikel ya koma Benchi.
Ya zuwa yanzu, an kiyasta Mikel Obi zai kai farashin Yuro miliyan 15 a kasuwa kuma akwai yiwuwar  dan kwallon ya kara tsada idan ya haskaka a gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil a watan Yuni mai zuwa.

 

Olympiakos ta yi wa Manchester United sakiyar da ba ruwa

A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Olympiakos da ke Girka ya yi wa na Manchester United da ke Ingila sakiyar da babu ruwa bayan ya lallasa na United da ci 2-0 a wasan farko a gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai da aka fi sani da UEFA Champions League.
kwallayen da Alejandro Dominigue da kuma wacce Joel Campbell suka zura a ragar United ne suka ba kulob din nasu damar samun nasara a kan na United.  Shi dai Joel Campbell, dan kwallon kulob din Arsenal da ke Ingila ne wanda suka ba da shi aro (loan) ga kulob din Olympiakos.
A makwanni biyu masu zuwa ne ake sa ran za a gudanar da wasa na biyu a filin wasa na Old Trafford da ke Ingila.
Sai dai yadda wasan farkon ya gudana bai yi wa magoya bayan kulob din United dadi ba hasalima sun cire dai daga tunanin tsinana wani abu a wasa zagaye na biyu.
Tun farko a wasan farko kulob din Borussia Dortmund ne ya lallasa na Zenit St. Petersburg da ke Rasha da ci 4-2.