✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A shirye nake in amsa tuhumar Magu —Malami

Ministan Shari'a ya ce ba ya shakkan bayar da shaida kan zargin Ibrahim Magu

Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya ce a shirye yake ya amsa kira, ya kuma gabatar da shaida kan dakataccen Shugaban Hukumar yaki da yi wa tattalin arziki ta’annati (EFCC), Ibrahim Magu, idan kwamitin bincike ya neme shi.

Hakan zai iya zama wani sabon babi a bincike da kuma zakulo ainahin gaskiyar zargin da ake yi wa Magu.

A ranar 8 ga watan Satumba, Magu, ta wasikar da lauyansa, Wahab Shittu, ya rubuta, ya bukaci Kwamitin Shugaban Kasa da ke binciken sa ya gayyaci Malami, domin gabatar da shaida tare da muhimman takardu kan zargin da ya gabatar wa shugaban kasa a kansa.

Malami, a wani shiri da ya bakwanta a Arise TV, ranar Laraba ya ce ba zai bayyana gaban kwamitin ba tare da bata lokaci ba saboda babu abin da ya ke shakka.

“Idan kwamitin Ayo Salami ya gayyaci Malami a matsayinsa na mutum ko a matsayinsa na Ministan Shari’a ya gabatar da shaida ko warware wata matsala ko duba na tabbatar da wani abu, Abubakar Malami zai je da zuciya daya bisa abin da doka ta tanadar ya gabatar da shaida”, inji malami