Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani ya ce a shirye kasarsa take ta hada kai tare da yin aiki da zababben shugaban kasar Amurka, Joe Biden.
Shugaban ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gudanar a gidan talabijin din kasar ranar Laraba.
- Iran ta zargi Amurka da kitsa yaki a duniya
- Zanen batanci ya kara tsamin dangantaka tsakanin Iran da Faransa
Ya ce, “Babban burinmu shine mu ga an cire takunkumin da aka kakabawa al’ummar Iran. Wannan burin kuma ya zo daidai da bukatar mutanen kasarmu,” inji shi.
Rouhani ya ce Iran a shirye take ta fara tattaunawa da Amurka, karkashin sharadin cewa Joe Biden zai dawo da yarjejeniyar makaman nukiliya ta 2015 ya kuma dage takunkuman da shugaba Donald Trump ya kakaba mata.
“Za mu yi duk mai yuwuwa wajen ganin mun dawo da kasarmu da mutanenta zuwa yarjeniyoyin tsakanin shekarun 2016 da 2017 ta hanyar cire takunkuman, a lokacin tattalin arzikin Iran na samun tagomashi,” inji shugaba Rouhani.
Daga nan sai ya yi kira ga abokan adawarsa kan kada su kawowa yunkurin nasa tarnaki.
‘Yan adawar Iran dai a lokuta da dama sun sha sukar manufofin Rouhani wadnda suka ce na goyon bayan kasashen yamma ne musamman a kan makamin nukiliya, suna masu cewa hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar Trump a zaben shugaban kasar a wancan lokacin.
A shekarar 2018 ne dai shugaba Trump ya janye daga yarjejeniyar makaman nukiliya wanda ya kunshi cirewa kasar takunkumin karya tattalin arzikin da aka sa mata muddin dai ta yarda ta daina sarrafa makaman.
Kazalika, Trump ya sake saka wa Iran din wasu sabbin takunkuman, lamarin da jefa kasar cikin wani halin matsin tattalin arziki mafi muni a tarihinta, wanda daga bisani annobar COVID-19 ta kara ta’azzarawa.