✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A shawo kan matsalar satar shanu

An shafe shekaru masu yawa ana  fama da matsalar satar shanu a kasar nan, wanda a yanzu matsalar ta gawurta har ta haifar da zubar…

An shafe shekaru masu yawa ana  fama da matsalar satar shanu a kasar nan, wanda a yanzu matsalar ta gawurta har ta haifar da zubar da jini. Matsalar satar shanu na barazanar haifar da karancin nama a kasar nan da kuma yunkurin kawo nakasu a bangaren noma tun da akan yi amfani da shanun ne wajen ayyukan gona.
Kodayake wannan matsalar ta zama gama duniya wadda ta sanya wadansu kasashen suka kirkiro dokokin musamman da hukunci mai tsanani da kuma jami’an sa idanu kan satar shanu duk don ganin an shawo kan al’amarin.
kungiyar Miyetti Allah ta Najeriya (MACBAN) ta ce a bara an kashe mata makiyaya 322, an kuma sace shanu fiye da dubu 60 a wadansu jihohin Arewacin kasar nan. Wannan zai karu idan aka hada makiyayan da aka kashe da kuma shanun da aka sace a jihohin Kudancin kasar nan. Haka rahoton bai hada da dukkan jihohin Arewacin Najeriya wadanda suke da makiyaya masu yawa ba.
Misali a Jihar Filato rikice-rikicen kabilanci da na addini sun sanya al’amarin ya fi kamari.
Lokaci ya yi da ya kamata gwamnati ta samar da wadansu shirye-shirye don ganin an gano bakin zaren al’amarin satar shanu. Ya kamata a nazarci yadda matsalar take, sannan a samar da nagartattun hanyoyin da za su kawo karshen kashe makiyaya da kuma satar shanu.
A kasar Scotland, an sace shanu 130 cikin shekarar 2012, sannan a farkon watanni 11 a shekarar 2013 an samu karuwar shanu 300, wannan adadin ya hada da yankuna 20 na kasar. Hakan ta sanya suka kira al’amarin da babbar ukuba a kasarsu, kasancewar ya gunguntar musu da tattalin arziki.
A kasar Scotland ba a samu rahoton rasa rayukan manoma ko makiyaya ba, don haka ba a samu tabbacin ko al’amarin ya gurguntar da noma a kasar ba. Sai dai shugabannin gargajiya a kasar sun ce ba za a alakanta satar shanu da rikicin iyaka ko kuma abu ne da ya shafi tsirarin jama’a ba, a’a, al’amari ne da ya shafi kasa baki daya.
Ya kamata a sake duba dokar satar shanu a Najeriya, sannan a yi doka ko samar da hukunci mai tsanani ga duk wanda aka kama da laifin satar shanu.
Baya ga haka ya kamata kungiyar Miyetti Allah da hukumar gandun daji su ware wani tallafin da za a rika ba duk wani makiyayin da al’amarin ya rutsa da shi. Za a iya wannan tsarin ne a karkashin kungiyar Miyetti Allah da Bankin Inshora da kuma tallafi daga gwamnati. Wannan tsari zai matukar taimakawa.
Matsalar ta zarce satar shanu da kuma kashe makiyaya domin al’amari ne da zai shafi lafiyar ‘yan kasa, domin shanun da aka sace akan yanka su sannan a kawo kasuwa.
Ana sayar da naman ne ba tare da lasisi ko ka’ida ba, idan kuwa haka ne ba za a tsabtace shi ba, wanda hakan zai yi sanadiyyar barkewar cututtuka, wannan abu ne da ya shafi jama’a don haka bai kamata a yi masa rikon sakainar-kashi ba.
Ya kamata mayankar da gwamnati ta amince da su su rika sanya idanu wurin tantance mahauta da kuma sauran masu sayar da nama don gano wadanda suke sayarwa ba tare da ka’ida ba.  
Matsalar satar shanu da kashe makiyaya ta yi kamari har ta sanya aka tattauna ta a Majalisun Tarayya.
Sace-sacen shanu da kuma kashe makiyaya kan faru ne a kauyuka da wuraren da ake noma da kiwo, kuma kowa yana da masaniyar akwai karancin jami’an tsaro a wadannan wurare.
Ya kamata ‘yan sanda su kirkiro dabaru da hikimomi da kuma hanyoyin magance satar shanu da kuma kashe makiyaya kafin al’amarin ya gagari kundila.