✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A saukaka wa manoman da suka yi asara

A makon da ya gabata ne Shugabar kungiyar Mata Manoma ta Najeriya, Farfesa Stella Williams ta bayyana cewa manoma a kasar nan suna fuskantar asara…

A makon da ya gabata ne Shugabar kungiyar Mata Manoma ta Najeriya, Farfesa Stella Williams ta bayyana cewa manoma a kasar nan suna fuskantar asara ga kayayyakin da suke nomawa, inda kashi 80 cikin 100 na kayan nasu ke lalacewa saboda rashin ingantattun kayan ajiya da kuma rashin ingantattar kasuwa. Ta ce a duk lokacin da kayan gona suka ki sayuwa, kafin lokaci suke rubewa, wanda haka ke haddasa wa manoma babbar asara.
Kamar yadda wasu masana harkar noma ke cewa, rashin dubaru da kayan ajiya, rashin ingantattun hanyoyin safarar kaya, rashin bunkasasshiyar kasuwa da sauran matsaloli daban-daban suna haddasa wa manoman Najeriya babbar asara. Musamman kuma kamfaonin sarrafa abinci da sauransu, sun fi ta’allaka ga kayan da suke shigowa daga kasashen waje.
Da za ka kai ziyara Kasuwar Mil 12 ta Legas, ko ka je Kasuwar ’Yan Lemo ta Zuba-Abuja, mutum zai gani da idonsa irin babbar asarar da manoman kasar nan suke tafkawa. Kusan rabin lemo da doyar da ake kawowa daga Biniwai, lalacewa suke yi, da zarar an kawo su kasuwa, kafin a kai ga sayar da su. Tuni da dadewa manoma ke korafi tare da kokawa da irin wannan asara da suke tafkawa a duk shekara, musamman ma yadda suke kasa mayar da kudin da suke kashewa wajen noma, balle ma a nemi wata riba. Ke nan suna faduwa ne kasa warwas a duk shekara. Wannan kuma babban hadari ne ga kasa, a ce manoma suna faduwa, domin kuwa ishara ce da ke nuna yiwuwar bayyanar yunwa, idan manoman suka jingine sana’arsu.
Bankin Duniya ma ya bayyana cewa, a duk shekara, manoma a Afirika suna asarar kayan gonar da suka kai kimar Dala biliyan hudu duk shekara. Irin wannan mummunar asara, tana sanyaya gwiwar manoma da sauran masu cin abinci ta wannan sana’a.
Manoma suna yin asara kusan a matakai daban-daban na killace kayan gonarsu, tun daga girbi, daukarsa zuwa rumbu da sauransu. Wasu manoman ma ba su da tabbatattar hanyar kai kayan nasu zuwa kasuwa, domin rashin hanyoyi ko kuma motocin safara. Duk da cewa a gwamnatocin baya sun dauki matakan rage asarar da manoma suke yi, amma babu shakka akwai bukatar a kara kaimi ta wannan fanni.
A 2011, Gwamnatin Tarayya ta gina manyan rumbuna guda 12 a sassa daban-daban na kasar nan, domin adana hatsi da wake da gari da sauransu. Haka kuma an sake gina wasu rumbunan guda 20. Amma duk da haka, manoma sun ci gaba da fuskantar asara, kuma an ci gaba da shigo da kayan abinci daga kasashen ketare, wanda haka ke haddasa zurarewar kudin shiga masu yawa daga kasar nan. Hatta cibiyoyin bincike sun yi ta kokarinsu domin nemo dubarun inganta harkar noma da adana kayan gona, sai dai mafi yawan abin da suka bincike yake karewa a dakunan binciken kawai, a yayin da matsalar ke ci gaba da wakana. Babu shakka ya kamata a samo hanyoyi na musamman domin tallafa wa manoma, yadda za su rage fuskantar asara. Ya kamata a sake bin kadin yadda bankuna ke bayar da bashin manona, a tsara hanyar da zai saukaka musu, domin su rage asara.
Ita kanta gwamnati, ya kamata ta dauki matakan samar wa manoma kudaden rance masu saukin ruwa, musamman za ta iya yin haka ta amfanin da dimbin kudaden fansho da ake tarawa, a samu wasu bankuna na musamman da za su gudanar da bayar da rancen, wanda zai zama mai amfani ga manoma. Rancen kuma ya kasance mai saukin biya da saukin ruwa. Su kansu kamfanoni masu zaman kansu, ya kamata su zuba jari mai yawa, domin tallafa wa harkar, ta yadda za su ci gajiyar al’amarin, kamar yadda su ma manoman za su ci tasu gajiyar, musamman ma kamar yadda manyan ’yan kasuwa irinsu dangote ke yi. dangote ya kafa kamfanin sayen amfanin gona kamar tumatir da sauransu kai tsaye daga manoma, inda yake sarrafa su a kamfanoninsa.
Ya kamata a ba dubarar nan ta hada ’yan kasuwar kayan goma da jawo hankalinsu su rika sayen amfanin goma kai tsaye daga manoma muhimmanci. Ya kamata gwamnati kuma ta inganta wutar lantarki domin samun hanyoyin adana kayan gona cikin sauki, a kuma samar da ingantattun hanyoyin safara, musamman a inganta da samar da jiragen kasa, domin saukaka harkokin safara.