✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A sake duba dokar fansho

A makon jiya ne kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa da na wakilai kan ma’aikata da kuma fansho suka gabatar da rahoton kwamitin a zauren…

A makon jiya ne kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa da na wakilai kan ma’aikata da kuma fansho suka gabatar da rahoton kwamitin a zauren majalisar wakilai. Makasudin zaman kwamitin don a sake duba dokar fansho ne da a aka yi a shekarar 2004. Sai dai tun ba a je ko’ina ba har wadansu ’yan majalisar sun fara zargin akwai lauje cikin nadi dangane da rahoton.
A sherarar da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta fitar da kudurin gyara dokar fansho ta shekarar 2004, inda ta bukaci a rage shekarun sanin makamar aikin daga shekara 20 zuwa 15 kafin a kai ga rike mukamin Babban Darakta a Hukumar Fansho ta kasa. Wadansu sun ba da shawarar a rage shekarun zuwa 10. Hakan ya sanya wadansu ’yan majalisar suka kalubalanci kudurin, inda suka ce ana so a yi wannan gyaran ne don a share wa jami’ar da take rikon kwarya a hukumar wato, Misis Chinelo Anohu-Amazu hanya don ta zama darakta ba wai ta riko ba. Misis Anohu-Amazu ta fara aiki a shekarar 1998, idan kuma aka ce za a bi tsarin dokar hukumar fansho, to ba ta kai shekara 20 na sanin makamar aikin da ake bukata kafin a nada ta mukamin babbar daraktar hukumar ba.
Rahoton kwamitin hadin gwiwar ya ce bai kamata a rika amfani da yawan shekarun sanin makamar aiki kafin a nada mukamin babban darakta a hukumar fansho ba. Kwamitin ya sake bukatar a kara wa’adin mukamin daga shekara 4 zuwa 5 ba kamar yadda aka tsara a shekarar 2004 ba.
Kodayake tuni zauren majalisun (na dattawa da na wakilai) suka yi watsi da wannan rahoton bayan wadansu mambobin kwamitin sun ce an yi amfani da sa-hannunsu na bogi ne, domin a cewarsu ba su sanya hannu a rahoton ba.
A ranar 6 ga Nuwamba, 2013 aka gabatar da rahoton a zauren majalisar dattawa, inda Shugaban Majalisar Dattawa, Dabid Mark ya ce akwai nakasu dangane da rahoton, sannan ya fada wa shugaban kwamitin Sanata Aloysius Etok ba za a amince da rahoton ba tare da dukkan mambobin kwamitin sun sa-hannun ba. Ko makon jiya ma wadansu daga cikin ‘yan majalisar wakilai sun ce ba su sanya hannu a rahoton ba.
Faruwar hakan ya sake sanya ayar tambaya a kan yadda ake gudanar da al’amara a majalisar tarayya. An sake waiwaitar duba dokar ne ba wai a kan wadanda suka yi ruf-da-ciki a kan dukiyar ma’aikata ko yadda za a inganta hukumar fansho ba, an yi ne kan zargin ana so a share wa wadansu fage ne don su kai ga hawa mukamai.
Ya kamata a samar da dokokin da za su rika inganta rayuwar jama’a daga lokaci zuwa lokaci ko kuma bisa ga halin da ake ciki. Sabon tsarin fansho bai jima ba domin bai kai shekara 20 a Najeriya ba.  Idan kuwa sai an samu shekarar sanin makamar aiki 20, to babu wanda ya cika ka’idar zama babban daraktan hukumar.
Kodayake yawancin dokoki a Najeriya ba ana yinsu don su taimaki talakawan kasa ba ne, ana dai yinsu don a taimaki wadansu tsiraru ne, ko don cim ma wani buri, don haka abubuwan da kwamitin hadin gwiwar ya yi ya bayyana akwai kura-kurai da gyare-gyare. Idan har za a ce za a rika yin dokokin don wadansu manufofi ne kawai, idan wadannan manufofi suka canza yaya za a yi ke nan?
Wannan ya sake dora majalisar tarayya cikin wani ma’aunin da ke cike da alamomin tambayoyi dangane da ayyukan da ake ba duk wani kwamiti a majalisar.  
Canje-canje a tsarin fansho babban al’amari ne, don haka ya zama dole a yi abin da za a rika cewa kwalliya ta biya kudin sabulu, ba wai a rika alla-wadai ba.