✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A rika hukuncin kisa ga mai almudahanar Naira biliyan guda

A kokartin da ake yin a yaki da cin hanci da rashawa, lokaci ya yi da mutane za su shiga taitayinsu, musammman ma ganin yadda…

A kokartin da ake yin a yaki da cin hanci da rashawa, lokaci ya yi da mutane za su shiga taitayinsu, musammman ma ganin yadda lamarin ke karya mana tattalin arzikin kasa. Idan ba ka yi ko ba ki yi sata ba, sannan ba ku kauce wa biyan harajin kasa da ya rataya kanku ba, lallai al’amura za su kyautatu a kasar mu, har mu zamo abin kwatance a faxin Afirka.

Ya kamata mutane su san cewa wannan yaki da ake yi kan cin hanci da rashawa duk kokari ne na shawo kan massu haurewa da kuxin da za a yi mana ayyukan raya kasa, waxanda idan ba a yi sub a, to mun koma baya. Tunda muna bukatar asibiti da tituna da hasken wutar lantarki. Matsalolin da rashawa da cin hanci suka haifar wa kasar suna da ximbin yawa. Don haka a yi takatsantsan. Matukar ba mu dakile wannan mummunar xabi’a a wannan lokaci ba, to al’umma za ta wahala.

Sannan ya kamata a ja kunnen alkalai domin wasu daga cikinsu bakinsu xaya da manyan barayin kasa. Wannan ne dalilin da ya suke tare da haxin bakin wasu lauyoyin ake jan shari’o’i ba tare da an yi hukunci ba, tsawon shekaru. Shari’ar tsohon gwamnan Jiha ta ma ya kamata a kawo karshenta ya san matsayinsa, gidan yarin kirikiri, Kurmawa ko kuma gidan yarin Kyawa, inda aka ajiye shi kwanakin baya da ya yi wata katobara. Idan so samu ne ma a sake garanbawul a tsarin shari’a a Najeriya.

Tabbas gwamnati na yin abin da ya dace wajen yakar cin hanci a Najeriya. Nan gaba abin da talaka zai fi mararinsa shi ne ya ga cewa an yanke wa wane xaurin shekaru goma, wane shekaru talatin ko arba’in. Wancan kuma hukuncin kisa ta hanyar rataya, wane kuma hukuncin kisa ta hanyar harbin bindiga. Idan Najeriya ta zama haka to nan gaba ko tsintuwa za mu rika tsoron xauka, ballantana dukiyar al’umma. Sannan muna so a yi dokar da za ta samar da hukuncin kisa ko na xaurin rai-da-rai ga duk wanda aka samu da almundahanar Naira biliyan xaya ko sama da haka.

08100229688/09073801967 seer ya’aky <[email protected]