✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A Rayuwa: Mu gode wa Allah a halin da muke ciki

Ya ku ma’abuta bibiyar Sinadarin Rayuwa, Assalamu alaikum, da fatan al’amura suna tafiya bisa dacewa. A yau kuma tambihi za mu yi wa juna, dangane…

Ya ku ma’abuta bibiyar Sinadarin Rayuwa, Assalamu alaikum, da fatan al’amura suna tafiya bisa dacewa. A yau kuma tambihi za mu yi wa juna, dangane da al’amuran rayuwarmu ta yau da kullum, cewa lallai ya kamata mu kasance masu yin godiya ga Allah, a duk yanayin da muka samu kanmu, domin kuwa duk rintsi, duk wahala, idan muka kwatanta da rayuwar wasu, za mu ga cewa muna cikin ni’ima da baiwar Allah.