Ranar Alhamis da ta gabata, 21 ga watan Nuwamba, rana ce ta bakin ciki a Jihar Adamawa, domin a ranar ce ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi wa mutum 80 kisan gilla, da kuma kisan rashin imani da wasu ‘yan ta’addan Bachama suka yi. Wadannan lamarin da suka faru a kusan lokaci daya, sun nuna matukar rashin imani, da kuma yada wasu suka mayar da ran mutum ba a bakin komai ba.
Inda barnar ta fi muni shi ne garin Mubi, a Arewacin Adamawa, inda mutum 50 suka mutu bayan wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam a cikin masallaci. Yadda abin ya faru shi ne, wani wanda ake zargi dan Boko Hara ne ya lallaba ya shiga cikin masallacin Madina da ke kusa da Yelwa da misalin karfe 5 na safe. Wanda ake zargin ya yi shiga ne kamar masallaci, sai ya tayar da bam din da ya daura a jikinsa. Makusanta masallacin sun ce sunga gawarwaki da yawa, kuma sun ga wadansu da suka jikkata sosai bayan bam din ya fashe.
Harin na Mubi shi ne mafi muni a wannan shekarar, kuma daya daga cikin mafi muni tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi ragamar mulki a shekarar 2015, kuma ya canja yadda ake yaki da ‘yan kungiyar na Boko Haram. Harin ya zo a lokacin da sojojinmu suke matukar kokari kuma suke samun galaba a kan ‘yan ta’addan. Kuma wannan harin na Mubi ya sa wadanda aka kashe a irin rikice-rikicen Boko Haram sun kai kusan 300 a wannan shekarar, kamar yadda hukomomin jin kai suka fada.
Duk da cewa Boko Haram na bangaren Abubakar Shekau da na Abu Mus’ab Albarnawi sun dauki alhakin wannan harin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma ya yi Allah wadai da harin, sannan kuma ya ce gwamnatinsa za ti yi duk mai yiwuwa wajen magance ‘yan Boko Haram a Jihar Adamawa da ma yankin Arewa maso Gabas.
Gwamnan Jihar Adamawa Mohammed Jibrilla Bindow shi ma ya ce harin akwai rashin hankali a ciki. Wannan bayanan da suka fito cikin sauri daga Shugaban kasa da gwamnatin jiha abin a yaba ne, amma jami’an tsaronmu da bangaren binciken sirrinsu dole su kara kaimi. ‘Yan banga suma dole su kara dagewa wajen lura da wajaje masu muhimmanci kamar wajajen ibadu da kasuwanni domin kiyaye sake aukuwar irin wannan harin na rashin hankali.
Yankin jihohin Borno, Yobe da Adamawa suna fuskantan ci gaba da hare-hare, musamman na kunar bakin wake, domin yanzu Boko Haram ba ta da karfin da za ta iya kwace gari ta rike garin. Harin garin Mubi, wanda gari ne na kasuwanci da ke da iyaka da Kamaru, wani ci baya ne, amma ba na dindindin ba. Boko Haram ta taba kwace garin a shekarar 2013, inda suke mayar da sunan garin ‘Madina’, amma rundunar sojin Najeriya ta kwato garin bayan shekara daya, wanda ya sa mutanen garin suka dawo. Don haka duk abin da ya kamata ayi domin a kiyaye garin, ya zama dole a yi domin a kiyaye su.
Hakanan kuma shi ma kisan mata da kananan yara 30 ‘yan kabilar Fulani da ‘yan ta’addan Bachama suka yi a Numan da ke Adamawa shi ma abin Allah wadai ne. marasa hankalin sun shigo suna wake-waken yaki suka kai farmaki kauyen Shafaran, Shawal, Gumara, Kikam da Kadamto a lokacin da mutanen kauyukan suka fita neman abinci. Suka kashe mata da kananan yara da adduna da wukake ba tare da tausayi ba. Shugaban kungiyar Miyetti Allah ta (CATBAN) na yankin Arewa maso Gabas, Mafindi Danburam ya ce an kashe sama da Fulani 60. Sannan wadanda suka kai harin ‘yan garin ne wadanda suka dade suna daukan alwashin yin hakan.
Rikici a Numan a tsakanin wadanda suke kiran kansu ‘yan garin da makiyaya ya sha faruwa a ‘yan kwanakin nan. A shekarar 2013, Gwamnatin Jihar Adamawa ta tsige Hamma Bachama Fredy Sodity Bango saboda zargin rashin gaskiya a rikice-rikicen da ke wakana a garin, amma akwai sauran aiki a gaba. wannan ya sa ya kamata a bibbiyi asalin abin da ke janyo rikicin daga tushe, sannan a magance su.
Wannan kisan na kwanan nan akwai rashin imani da rashin hankali a ciki, kuma bai kamata a yi shiru ba. Rashin girmama dan Adam ne wannan da rashin girmama kundin tsarin mulkin Gwamnatin Tarayyar Najeriya wanda ya bayar da dama ga kowa ya zauna a duk inda yake so.
Kisan gillar Numan ya tunatar da irin kisan gillar da wadannan mutanen suka yi a karamar Hukumar Sardauna ta Jihar Taraba a farkon wannan shekarar. Dole a nemo wadanda suka yi wannan kisan, kuma a musu hukunci daidai da laifinsu domin ya zama izina ga wadanda suke da niyyar aikata irin wannan kisa nan gaba.