✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A kawo karshen kashe-kashen nan haka nan

A kwanakin baya kusan mutum hamsin suka rasa rayukansu, wadanda suka hada da yara da mata da tsofaffi, a yayin da wasu ’yan bindiga suka…

A kwanakin baya kusan mutum hamsin suka rasa rayukansu, wadanda suka hada da yara da mata da tsofaffi, a yayin da wasu ’yan bindiga suka kai hari zuwa wasu kauyukan karamar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna. ’Yan bindigar wadanda ya zuwa yanzu hukuma ba ta tabbatar da ko su wane ne ba, rahoto ya tabbatar da cewa sun far wa kauyukan Fadan Karshi da Fadan Karshi Daji da Unguwar Ganye da safiyar ranar 17 ga Satumba, inda a sakamakon haka daruruwan mutane suka gudu daga gidajensu domin ceton rai. Mataimakin Shugaban karamar Hukuma, Mista Bulus Anzah ya ce mutum 12 aka kashe a Fadan Karshi, 30 a Fadan Karshi Daji, sannan kuma aka kashe 7 a Unguwar Ganye.
Da ma a can baya, wadannan yankunan sun yi kaurin suna wajen tashe-tashen hankali. Tun daga Yuli na bana, an samu faruwar rikice-rikicen kabilanci guda 12, inda mutane sama da 300 suka rasa rayukansu. Dalili ke nan Mista Bulus ya nuna alhininsa da faruwan wannan al’amari, inda ya ce abin ya wuce kima kuma an kasa magance shi. Kodayake a wannan harin na baya, wasu sojoji sun yi kokarin dakile shi, har ma suka samu raunuka, aka kai su asibitin sojoji na Kaduna, wanda haka ke nuna irin yadda al’amarin ya munana.
Akwai wasu da ke ganin beken yadda Gwamnatin Jihar Kaduna ke daukar matakai wajen sasanta al’ummomi daban-daban. Misali, a kwanakin baya da Gwamna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya ziyarci yankin, da nufin jajanta musu kan rashin rayukan da suka yi a sanadiyyar wannan hari, mata da dama suka fito suna zanga-zangar nuna masa rashin gamsuwa, suna fadin cewa ya je yankin ne kawai da nufin kamfen din siyasa. Jami’an da suka yi masa rakiya ne ma suka rika bayyana cewa ba kamfen ne ya kai shi ba.
A yayin da yake ganawa da ’yan jarida, Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Kaduna, Mista Ben Bako ya ce tun farko, ’yan asalin yankin Sanga ne suka fara wannan rikici na bayan nan. Kamar yadda ya ce, yadda mutanen kauyen suka far wa al’ummar Fulani, shi ya haifar da harin ramuwar gayya. Wannan shi ya haifar da daukar fansa ga kan Fulani da al’ummar garin suka sake yi, wanda kuma al’amarin ya ki ci, ya ki cinyewa, yake ta faruwa a kai-a kai.
Idan dai har wannan bayanin na Mista Bako ya tabbata gaskiya, to kuwa lallai akwai bukatar a dauki kwakkwaran matakin shawo kan al’amarin, musamman ta hanyar sasanci tsakanin mabambantan kabilun da ke zaune a yankin. Wani abin lura kuma shi ne, zai yi wuya a magance matsalar nan ta hanyar girke dakarun soja ko ’yan sanda a kauyukan yankin na Sanga, domin kuwa gidaje suna a warwatse ne, ba wuri guda suke a dunkule ba. Ga kuma barazanar da ’yan ta’adda ke kawowa, wanda haka zai sa a samu wahalar samar da jami’an tsaro masu yawa a yankin, domin magance irin wadannan hare-hare da ke faruwa a yankin.
Ya dace gwamnatin jihar ta dauki matakan da suka dace wajen cusa wa mabambantan al’ummomin kauna da aminci ga juna. Ta yi kokari wajen ganin ta samar da zaman lafiya tsakanin al’ummomin yankin, ta yadda za su zauna cikin lumana. Gwamnatin za ta samu nasara, musamman idan ta nemi hadin kan dattawan yankin, ta sanya su gaba wajen kawo sasanci tsakanin kabilun ba tare da nuna son kai ko bambanci ba. Haka kuma, ya dace ta hada hannu da shugabannin al’umma da malaman addinai na yankin wajen tabbatar da kawo maslaha. Ta haka ne za a samu nasarar kwantar da hankalin al’umma kuma a magance rashin jituwar da ke faruwa tsakaninsu.
Su kuwa wadanda aka kama da laifin tayar da wannan hargitsi na baya-bayan nan, lallai ne a tabbatar da an hukunta su. Domin kuwa bai dace ba a ce za a sanya ido ana kashe al’umma, ana lalata dukiyoyi ba tare da daukar matakin da ya dace ba. Haka kuma, ya dace Gwamnatin Jihar Kaduna ta duba yiwuwar biyan diyya ga wasu al’umma da suka fuskanci rashi ko asara na rayuka ko kuma shanu da sauran dukiyoyi, a sakamakon wannan rikici na baya-baya. Daga karshe, lallai ne gwamnati ta yi duk abin da za ta yi, domin ganin ta kawo karshen rikice-rikicen da suka zama ruwan dare kuma suke yawan faruwa a sassan karamar Hukumar Sanga.