✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A katafaren gida ake tsare mu a Najeriya – Zakzaky

Jagoran kungiyar IMN ta ’Yan Shi’a a Najeriya, Ibraheem Zakzaky, ya bayyana dalla-dallar halin da shi da iyalinsa suka kasance a Najeriya lokacin da ya…

Jagoran kungiyar IMN ta ’Yan Shi’a a Najeriya, Ibraheem Zakzaky, ya bayyana dalla-dallar halin da shi da iyalinsa suka kasance a Najeriya lokacin da ya je Indiya neman magani. A wani bidiyo da jaridar The Cable ta fitar, an ji Sheikh Zakzaky yana ba wani jami’in gwamnatin Indiya labarin yada gwamnatin Najeriya ta tsare su shi da mai dakinsa. “Na yi kusan shekara hudu a tsare; a wani katafaren gida nake. Kai bari ma in shaida maka, makwabcinmu shi ne Shugaban Majalisar Dattawa; a wannan gidan alfarma, na samu damar watayawa.Haka lokacin da suka dauke ni zuwa Kaduna, a mafi kyan wuri nake – Unguwar GRA. A nan ma wani gida ne cike da kayan alatu da manyan dakuna, kuma ina cikakkiyar watayawa.

“Ba a taba tsare ni da ’yan sanda ba; sojojin da ke tsarona suna tsayawa ne a wajen gida. Haka suke yi. Amma  lokacin da muka zo nan (Indiya) tamkar gidan kurkuku aka kawo mu,” inji Zakzaky a bidiyon.

Wannan bayanin ya zama akasin abin da jama’a suke tunani cewa an tsare jagoran Shi’ar ne a gidan yari  tare da mai dakinsa tun karshen Disamban 2015.

Zakzaky ya ba da wannan labari ne ga wannan jami’in kasar Indiya wanda aka gani a gefen gadonsa lokacin da yake asibitin Indiya domin a duba shi. Daga baya hakan bai yiwu ba, ya dawo gida.

A baya, Gwamnatin Tarayya ta yi ikirarin cewa duk wata tana kashe Naira miliyan 13  kan kula da Zakzaky, kamar yadda Ministan Labarai Alhaji Lai Mohammed ya ce.