✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

A kashe mutum, an kona gidaje 22 a Zangon Kataf

An kona gidaje 22 bayan an kashe mutum daya a wani hari da aka kai wa kauyen Manyi Shishok da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf…

An kona gidaje 22 bayan an kashe mutum daya a wani hari da aka kai wa kauyen Manyi Shishok da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna.

Hari na hudu ke nan da aka kai daga ranar Lahadi zuwa Laraba a  Masarautar Atyap da ke karabar hukumar.

Harin na karshe an kai shi ne a ranar Talata da dare kuma har yanzu ba a kai ga gano ko su wane ne maharan ba.

Shugaban Kwamitin Tabbatar da Tsaro da Zaman Lafiya na Karamar Hukumar Zangon Kataf, John Bala Gora, ya ce maharan sun far wa kauyen ne da misalin karfe 9 na dare.

Gora ya yi tir da harin sannan ya bukaci jami’an tsaro da su kara kaimi wajen shawon matsalar tsaron da ke addabar yankin.