A karon farko an ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari snaye da takunkumin kariyar cutar coronavirus a bainar jama’a.
An ga Buhari sanye takunkumin ne a lokacin ziyararsa ta farko zuwa kasashen waje tun bayan bullar cutar ta coronavirus.

Ya kai ziyarar ta farko ne kasar Mali inda shugabanni daga Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) ke tattaunawa domin kawo karshen rikicin siyasa da ya barke a kasar.

Taron na birnin Bamako na gudana ne karkashin jagorancin Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mahamadou Issoufou.

Rikicin siyasar ya samo asali ne daga soke zaben wasu ‘yan majalisar Mali wanda wasu kungiyoyi suka zargi Shugaba Keita ta hannu a ciki.

A farkon makon nan ne Buhari ya saurari rahoton rikicin daga Jakada Musamman, tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan a Abuja.
