Rundunar ’yan sanda ta jihar Kano ta ce mutanen da suka yi fatali da dokar zaman kulle da gwamnati ta kafa suka jagoranci sallar juma’a a masallatansu za ta gurfanar da su a gaban kotu.
Kakakin rundunar ASP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka ga manema labarai a ofishinsa.
Kiyawa ya kara da cewa galibin mutanen da aka kama su 15 mutanen gari ne suka taimaka wa ’yan sanda wajen kama su.
- A karo na farko ba a yi sallar Juma’a ba a Kano
- Dokar Hana Sallar Juma’a: An kama Limamai biyu a Kaduna
Yawancin wadanda Aminiya ta tattauna da su a cikin mutanen sun bayyana cewa ba su da masaniya game da tanade-tanaden dokar – a zatonsu dokar ta wajabta zaman gida ne kawai ba ta hana yin sallar Juma’a ba.
Malam Hamisu Ahmad, limamin masallacin salloli biyar na unguwar Hausawa a karamar hukumar Tarauni, ya bayyana cewa, “Ni gaskiya na zaci dokar ta shafi masallatan Juma’a ne kawai shi ya sa muka yi sallarmu ta Juma’a a masallacinmu da muke yin salloli biyar. Kuma mun gudanar da sallarmu tare da yin huduba”.
Shi ma wani da ya jagoranci fiye da mutane 200 sallar Juma’a a garin Garun Ali, Malam Ado Gambo, ya bayyana cewa bai san da dokar ba gaba daya don haka ya nemi a yi masa afuwa.
Sai dai rundunar ’yan sandan ta ce ba za ta saurara wa limaman ba domin hukuncin da za yanke musu ya zama izna ga na baya.
Gwamnatin jihar Kano ce dai ta sanya dokar hana zirga-zirga a fadin jihar a kokarinta na hana yaduwar cutar coronavirus a fadin jihar.