Alhaji Bawa Garba (ABG) suna ne da ya yi tambari a fannin kasuwanci da aikin jarida, musamman na talabijin. A tattaunawarsa da Aminiya kan rayuwarsa ya ce tun yana dan shekara tara ya fara bin mahaifinsa harkokin kasuwanci a kan jaki:
Aminiya: Yaya aka yi ka fara kasuwanci?
Na fara kasuwanci ne tun ina da shekara tara ba tare da jari ba. Mahaifina, Garba dan kasuwa ne daga Garkida, dan kabilar Babur ne. Mahaifiyata Jero kuma Bafulatana ce daga karamar Hukumar Song.
Na fara bin mahaifina harkokin kasuwanci ne tun ina dan shekara tara a kan jaki muna kai farar kasa zuwa Garkida.
Mahaifina yana kai wa Turawan Mishan ne farar kasa kuma hakowa muke yi. Garkida ta yi fice a wancan lokaci kuma mutane daga Kano da kasar Kamaru ke zuwa garin. Ina yi maka maganar1935 ke nan ko fiye. Turawan Mishan sun iso Garkida don fadada Makarantar Sakandare da ruwan sha a Biu.
Akwai wata gada da ta raba iyaka a 1935, Garkida na karkashin Jihar Borno amma daga baya muka dawo karkashin tsohuwar Jihar Gongola (yanzu kuma Adamawa). Idan mahaifina ya fita da jakin nakan bi shi mu je mu kwaso farar kasa wadda yake sayar wa Turawa a yankin da sauran yankuna.
A lokacin ina makarantar Musulunci a garin Biu inda aka tura ni tare da Sarki na yanzu Mai Mustapha. Ina da kiriniya a lokacin, ina yaro sai in ki zama in yi karatu saboda haka sai na koma gida Garkida. Marigayi Lamidon Adamawa Alhaji Usman Borkono da kawuna da ke cikin majalisa sai kuma Turawan Mishan da ke zaune a wani yanki na Garkida. Muna zaune ne a Unguwar Fulani.
Iyayenmu ba su son sanya mu a makarantar boko saboda suna tsoron Turawan Mishan za su samu yi rida. ýAmma alakar da ke a tsakanin mahaifina da su wadda ta samo asali daga kasuwancin farar kasa ta sa ya ga bai dace in yi karatun addini kadai ba don haka sai ya sani a boko tare da wata yarinya wadda ta rasu. Ita ce matar tsohon Sakataren Gwamnati Maccido Dalhat wanda shi ma ya rasu. Idan lokacin karatun addini ya yi, ni da wannan yarinya za a ce mu fita domin mu biyu ne kawai Musulmi duk sauran daliban Kiristoci ne. Haka muka fara a 1952.
Bayan shekara daya sai suka fada mana cewa suna son bude wasu makarantu domin su nuna wa Fulani da Hausawa muhimmacin kai ’ya’yansu makarantar boko. Ba mu biyan ko kwabo su ke biyanmu.
Na fara nawa kasuwancin ne da jarin da bai kai Naira dubu daya ba. Ina sayar da kayan masarufi a Garkida. Nakan tafi makarantar firamare idan na dawo kuma in ci gaba da kasuwancina. Sannan ina ci gaba da bin mahaifina zuwa harkokin kasuwancinsa.
Ta haka na zama dan kasuwa har na samu damar ajiye wasu ’yan kudi. A 1959 aka ce mu tafi Yola lokacin ina cikin ganiyar karatuna domin na samu kyaututtuka masu yawa a fannin wasannin motsa jiki ciki har da kwallon kafa.
Na bar makarantar da nake a 1959 zuwa karamar Hukumar Girei ’yan kilomita kadan daga Yola. A nan ne na fara karatun babbar firamare. A nan kuma na fara wani sabon kasuwanci. Muna debo wa shugabaninmu ruwan su kuma gwamnati na biyansu sule 30 a wata.
Mu ma gwamnati na biyanmu sannan kuma a ba mu kayan makarant kyauta kuma a ciyar da mu. Lokacin da za mu tafi hutu sai na shiga motar haya a kan hanya sai in biya in gai da kakana. Saboda muna yara idan za mu yi tafiya sai mu ki wanka na kwana biyu saboda mu nuna cewa a babbar motar kwasar kaya muka zo.
A lokacin babu kwalta a kan hanyoyin a cikin motar nakan zauna a gaba domin in rika karbar kudin mota daga mutane. Ni kuma sai a ba ni nawa ladan daga wajensu, har da abokan karatuna da kuma shi kansa direban. Wadansu daga cikin abokan karatuna su ne Farfesa Gidado wanda ya yi Shugaban Hukumar UBEC.
A lokacin hutu ina da na’urar kallo-kallo wadda idan ka matsa ta sai ta rika nuna maka kasar Saudiyya da sauran wurare. A lokacin ina Yola Kawuna yakan tafi wurare a Gongola kuma tare muke zuwa wani lokaci. Idan yana tattauna lamarin siyasa tare da hakimi sai in tafi cikin garin Guni inda mafi yawan mutanen Musulmi ne.
Sai in rika nuna musu wasu wurare na kasar Saudiyya ina kuma tattaunawa da su ne da harshen Fulatanci su kuma su biya ni. Haka na yi a garin Yungur wanda a yanzu yake Jihar Taraba. Saboda rashin wayewa mata kusan a tsirara suke yawo, abin dariya. Ni kuma sai in rika nuna musu raye-raye a cikin na’urata sai in rika yi musu karin bayani cikin Fulatanci.
Sukan rataya ’yan sulallansu ne a wuya idan suka kammala kallo sai su cire kudi su biya. Ba su saba ganinsa ba don haka sai ’ya’yansu su rika rawa ni kuma ina fada musu cewa za a yi ruwan sama.
A lokacin da nake Girei na ci gaba da yin kasuwanci. Na fara sayar wa malamaina taba sigari har da shugaban malaman makarantar masu sha. Suna biyana idan sun karbi albashinsu. Wannan ya sa wani lokaci ba su hukunta ni koda na yi laifi domin duk wanda ya buge ni sai in hana shi bashi.
Ga shi kuma na iya kwallon kafa sosai a wancan lokaci saboda haka a duk lokacin da muke da wasa Hakiminmu sai ya fito da kujerarsa tare da sauran mutane da ke zuwa daga cikin gari da yamma saboda kallo.
Idan na daki kwallo sai su rika kirana BG ma’ana Bawa Garkida ba Bawa Garba ba. Nakan ji dadi matuka kan yadda nake wasa. A ranar kasuwa sai in tafi wajen kallo inda nake samun kudi. Yadda na ci gaba da kasuwanci ke nan.
Aminiya: Me kake yi da kudin da kake samu?
Ina cikin walwala saboda idan na fita kullum sai na dawo da shinkafa da doya wadanda ba kowa ke iya samunsu ba a yankin a lokacin. Sai in bai wa matar Kawuna.
Aminiya: Wa ke ajiye maka kudinka tunda a lokacin babu banki?
Ni nake ajiyewa, ba su da yawa amma suna da daraja.
A lokacin an zo za a dauki mutane aikin dan sanda a makarantar babbar firamare da ke Girei. An gwada mu kuma aka aminta cewa na dace. Haka aka kawo mu Kaduna. Abokin mahaifina Ibrahim Biu Minista ne a lokacin Sardauna yana zaune a Kaduna. Sai mahaifina ya ce in tafi wajensa. Na nemi inda yake na same me shi, sai aka ba ni aiki a Norted a matsayin akawu. Kamfanin kuma ya aika da mu karin ilimi.
Ke nan ba ka shiga aikin dan sanda ba?
Eh.
Me ya sa?
Saboda na fi sha’awar aiki a Norted shi ya sa na ki shiga aikin dan sanda. Na samu matsayi inda har suka ba ni mota kirar Baswaja wadda ke kai ni gida. A matsayina na mara mata a lokacin nakan tashi da misalin karfe 5 na Asuba kullum domin yin girki.
A lokacin an fara Yakin Basasa a kasar nan. A lokacin ne jaridar Sunday Times ta buga labarina cewa ga dan Arewa da ka yin aikin da ba kowane dan Arewa zai iya yi ba. Saboda a lokacin na shiga aikin sayar da jarida a Kaduna. A lokacin da kamfanin New Nigerian ya fara aiki. Ina sayar da jaridar da safe.
Nakan kira masu sayar da jaridu in raba musu kwafi kafin in tafi wajen aiki. Idan na kammala girkin safe na kuma raba wa masu sayar da jaridu jaridun sai in wuce kamfanin raba wasiku in cigaba da aiki saboda a lokacin babu ’yan Arewa da ke aikin kuma ’yan Kudu sun fara komawa yankunansu.
A lokacin da hakan ke faruwa sai na zo Layin Golko wanda ake kira Benin a yanzu a Kaduna inda na hadu da Ambasada Magaji Mohammed. Shi ne shugaba a wajen kuma suna neman ’yan Arewa da za su yi musu wasu ayyuka. Ina aiki a ofishin raba wasiku kuma an ba ni wani tsohon gida a Layin Benuwai inda na fara wata cibiyar domin koyawa ’yan Arewa aikin buga keken rubutu, wadanda za a aika filin daga. Daga baya wajen ya zama cibiyar kasuwancina inda nakan tashi da safe
in raba jaridu sannan in tafi ofishin raba wasiku da yamma in dawo cikin gari domin kula da ajujuwana da dalibai.
Cibiyar ko in ce makarantar ta bunkasa inda mutanen da ke da sha’awa suka rika yin tururuwa zuwa wurin. Wannan ne ya fara bude min ido kan yadda ake hulda da jama’a. Kawai sai hanyoyi suka kara buduwa gare ni, inda wani kamfani ya nemi in bar Norted in dawo wajensa. Sun ce za su kara min albashi. A lokacin ina zaune a cikin wani karamin daki ne kuma mahaifina ne ya kawo min matata.
Ta wace hanya ka rika samun dalibai da malamai a makarantar?
A’a ai da zarar ka fara wani abu labari yakan yadu. Game da malamai kuwa, ina da mutane kamar su Daramola da sauransu. Gwamnati na sane da makarantar ta ba ni amincewa a karkashin sashi na 10 na dokar ilimi ta Arewa lokacin Ahmed Kutigi ne Ministan Labarai.
Ko an dauki lokaci kafin a ba ka damar rika koyar da karatu?
A’a. Na je wajen abokina Magaji saboda suna neman mutane irina wadanda za su iya bude kasuwanci. Ahmadu Commassie wato mahaifin tsohon Shugaban ’Yan sandan Najeriya Ibrahim Commasie yana raba sababbin Baswaja ga matasa ba tare da ba da jinginar kadara ba wanda kuma za a biya bayan wani lokaci.
Kuma ni a lokacin ina da mota saboda haka ba na bukatar motar. Sai Commassie ya ce suna bukatar ’yan Arewa masu fasahar kasuwanci da za su bude asusun ajiya a banki saboda haka sai na je na bude asusun ajiya a Bankin Standard.
Manajan Bankin, Bature ne dan kasar Birtaniya kuma shi ya raka ni sabon ofishina da ke Titin Gombe. Kafin in samu motar da ke kai ni gida ina da babur kuma da shi nake gudanar da ayyukana. Kuma Kamfanin Gine-Gine na Arewa ya ba ni mota da kuma direba.
A 1967 zuwa 1968, ni ke biyan ma’aikata kudin aiki da albashi sannan in mai da sauran da suka rage. Na so aikin saboda da zarar na kammala biyan ma’aikata hakkinsu shi ke nan sai in yi tafiyata. A lokacin na riga na yi aure domin na yi aure a 1965. dana na na farko an haife shi a ran 16 ga Fabrairun 1966.
Duk harkokina a Kaduna suke, sai da na bar dakin da nake kwana ciki daya a Kaduna ta Kudu na koma gida Mai Lamba BZ 8 a Sardauna Cresent bayan na yi aure. A lokacin harkokina na ci gaba da bunkasa saboda haka a 1968, wani kamfani mai suna Nabesty Press Limited suka shigo. Zan tafi makaranta idan na dawo in ba su mujallu. Haka ina da littattafai da yawa na Lenin a bayan mota wadanda nake rabarwa.
’Yan kasar Rasha na cike da farin ciki ka san Rasha na adawa da ’yan Jari-Hujja.
Su ’yan Gurguzu ne, saboda haka sai Ofishin Jakadancin Amurka suka fara nemana cewa za su karamin kudin albashi idan har zan daina harka da kasar Rasha. Su kuma Rasha sai suka dauke ni zuwa Mosko babban birnin kasarsu a 1969 wannan ne karon farko na wayewata.
A lokacin da nake Mosko na fara ganin kankara sanyi daga nan suka dauke ni zuwa birnin Leningrad inda na fara ganin dogayen bene. Idan ka nemi kalllon bene sai hularka ta fadi.
Sau biyu ina zuwa kasar Rasha kuma komai na tafiya yadda ya kamata. Farfaganda na gudana yadda ya kamata kuma mutane na kara sanin Nobelty Press a duk fadin Arewacin kasar nan. Wannan ne farkon fara harkar jarida.
Saboda ina ganawa da manema labarai har zuwa 1975 ina cikin wannan harka dumu-dumu. An kammala Yakin Basasa a 1970, ina cikin harkokin kasuwanci da yawa hakan ya sa na zama cikakken dan kasuwa. Na bar aiki da kasar Rasha saboda matsi daga kasar Amurka saboda suna ganin kamar ina taimaka wa Rasha, saboda kare rayuwata.
Ina zaune a Kaduna lokacin da na sayi gidana na farko a kan Naira miliyan daya. Gida Mai lamba AF 4 Titin Paki, sai labari a yadu a gari domin a lokacin Naira miliyan daya makudan kudi ne. Na bai wa wani kanena, ya rasu.
Bayan ka yi watsi da Amerikawa me ya faru?
Sai na kafa nawa kamfanin kuma muka ci gaba da kasuwanci. Lokacin da marigayi Murtala Mohammed ya kirkiro karin jihohi kuma ya kirkiro Jihar Arewa maso Gabas sai aka ba ni kwangilar samar da kayayyakin ofisoshi da kekunan buga rubutu. Haka na kasance wakilin Kamfanin UTC da ke Legas, a nan ne na kara fahimtar Jihar Legas shi ma babbar harka ce a gare ni.
Kwangilar da aka ba ni na kayayyakin ofis ba ta kai Naira miliyan daya ba amma sai da ta zama abin magana a gari. Bankina wato Standard wanda yanzu ya zama First Bank sun nemi in saka hannu domin su samar da kayayyakin a kan su za su ba ni kudin amma sai na ki.
Na ce da su ba ni son bashin banki, daga nan ne Commassie ya shigo. Ya fada min cewa “Kai matashi ne kada ka damu ka yi abin da suka ce da kai. Muna son ka ci gaba ne.” Ya fada min haka ne saboda an fada masa ni dan Arewa ne. Commassie ya shawo kaina har na amince, suka yi aikin. Suka mayar da ni dila kai-tsaye saboda aikin da na samar.
Manajan wanda Bature ne ya ba ni bashi wanda banki ne ke shirye su biya, hakan ba ya faruwa a yanzu. A lokacin da suka kammala har suka nuna min abin da ke cikin asusun ajiyata ban yarda ba. Da suka aika min da ribata a yanzu ba zan iya tunawa da yawan kudin ba amma dai kam makudan kudi ne. Na kasa tabawa har sai da na koma gida na nuna wa iyayena domin su sanya min albarka. Kamar yadda na yi lokacin da aka fara ba ni albashi na farko.
Duk lokacin da aka ambaci ABG abin da ke zuwa zukatan mutane shi ne taurarun dan Adam. Yaya aka yi ka shiga wannan harka?
Na fada maka na shiga harkoki da yawa. Lokacin da na ga Kasuwar Duniya ta Kaduna ke bunkasa sai na gayyaci mahaifiyata ta mika wa Shugaban kasa Shehu Shagari akwatin talabijin. Rana ce da ba za ta taba mantawa da shi ba, ta yi matukar mamaki. Harkar talabijin din na ci gaba da bunkasa, kuma canja sunan zuwa ABG ya taimaka min matuka. Daga nan na fara tunanin yadda zan kare kasuwancina sai tunanin tauraron dan Adam ya fado min. Na tafi birnin Washington FC tare da dana Musa, muka wuce Atlanta cibiyar CNN na fada musu ina bukatar in taimaka musu wajen kara yada Kamfanin Talabijin na CNN a Najeriya. Suka ba ni dama kamata ya yi in biya kudi kafin su ba ni, amma sai suka ba ni kyauta. Da na dawo gida sai na fara yin dish a lokacin ne aka soma Yakin Tekun Fasha, sai cinikin ya bunkasa.
Ina yin manyan dish a ma’aikatar da ke Kaduna ta Kudu, a lokacin ina zuwa duk bikin baje-koli na kasuwannin duniya. Wata rana sai na ci karo da karamin dish da ake sayarwa Naira 14,000 haka ya sa muka sanya sunan ABG ko’ina. Na sayo dish din na kaddamar da shi a Legas mutane na ta mamakin yadda karamin dish zai yi inganci.
Ibo suka sanya ido a kai kuma mutane na ta tururuwar saye. Suna mamakin yadda dan Arewa zai iya wannan. ’Yan Kudu sun samu saya daga inda nake sayen na’urar, suka shigo da su inda suka rika yin marar inganci a Kasuwar Aba. dana injiniya ne ya ce da ni mu koma bikin baje-koli na Stuttgart domin samun wata na’urar da za mu iya kauce wa masu neman lalata mana kasuwanci. A Jamus aka ba mu labarin wata na’urar na sayo na sa amma ba ni da dikoda, sai na fara talla mutane su saya daga wurinmu muka ce duk wanda bai saya a wurinmu ba, to, za mu rufe tashoshinsa.
Suna ta mamakin yadda za mu iya yin haka da muka samu damar yin haka ga satilayit din mu sai muka fara rufe tashoshinmu da mutane suka lura abin da muke fadi za mu yi mun fara sai suka fara zuwa sayen dikoda. Muka fara samun riba tare da sayo wasu dikodojin da yawa. kalubalen da muka fuskanta da ’yan Najeriya sai da suka sake samun hanyar lalata wannan abu da muka yi bayan wasu ’yan shekaru. Sai na fara tunanin abin yi domin in samu kariya daga gare su. Ina cikin wannan hali ne gwamnati ta fito da dokar yin rajista ga kamfanoni masu harka irin tamu. Kafin in soma kasuwancin satilayit sai da na je wajen Shugaba Ibrahim Babanida domin neman izininsa. Ya aike da wasika ga Minista Akinyele domin ya ba ni izini. Saboda abin da nake yi ne aka kirkiro da Hukumar NBC.
NBC suka ce dole mu nemi izni daga Hukumar Talibijin ta kasa (NTA), a lokacin Muhammed Ibrahim ne shugabanta wanda yake a yanzu Hakimi. Ya kira ni domin sanin irin abubuwan da nake so in rika nunawa a na’urar satilayit dina. Na shaida masa, bayan mun fahinci juna sai ya rubuta wasika ga gwamnati cewa ba ya da matsala da aikina. Ka ji yadda aka yi na samu wannan izni kyauta. Ba don haka ba sai na biya Naira miliyan 10 a cikin shekara biyar kafin in samu takardar iznin yin aiki a Legas da Abuja da Kaduna da sauran jihohin kasar nan.
Abin da kawai ya karya ni shi ne da zarar mun samar da na’ura sai a samu wadansu su karya ko su lalata ta. Jiha kamar tawa ta Adamawa da wasu wurare ba su biya sai muka fara yin hasara.
Da DSTb suka shigo Najeriya domin mu hada hannu mu yi aiki saboda na riga na samu masu bukata amma da muka zauna sai muka samu rashin jituwa kan farashi. Na shaida musu ba zan iya amfani da farashinsu a Arewa ba sai dai a Legas. Suka matsa kuma saboda yadda na fahinci harkar a Arewa sai na ki amincewa.
Sai na sa hannu a takardar yarjejeniya a kan farashin Legas kawai. Bayan wani lokaci suka bunkasa, da na amince dai sai dai kawai in rika barci al’amura na ci gaba da zuwa kurum. An ba ni lambar girmamawa ta Dokta a lokacin, mutane da yawa sun nemi ba ni lambobin yabo a kasar nan amma na ki. Wadda aka ba ni daga birnin Atlanta na kasar Amurka ce kawai na karba. Saboda na san ta gaskiya ce sai da suka je Kamfanin CNN suka nemi bayani a kaina kafin su ba ni lambar yabon.
Ni na kawo Peter Arnet daya daga cikin manyan Kamfanin CNN Najeriya a lokacin Sani Abacha. Lokacin matar Shugaban kasa na bukatar a san ta a duniya su kuma CNN na bukatar sanin dalilan da za sa su sa su ba ta wannan dama kuma ba su zuwa Najeriya saboda suna tsoron Abacha. Saboda haka sai suka shirya cewa Peter Arnet ya zo Najeriya amma ni zan je in tarbe shi a kasar Ghana.
Ya shigo ya zanta da Maryam Abacha a kan ayyukanta. Aka aika da kaset din hirar zuwa Kano daga nan aka aika da shi Landan domin a nuna a CNN da sauran kafafen watsa labarai na duniya.