Kungiyar Dalibai Musulmi ta Najeriya, (MSSN), Shiyyar Jama’a da ta kunshi Kananan Hukumomin Jama’a da Kaura da Jaba da Sanga a Jihar Kaduna, ta bukaci gwamnatin jihar ta kara inganta tsaro a makarantun da ke Kudancin Jihar saboda barazanar da dalibai kan fuskanta a duk lokacin da aka samu hatsaniya ko jita-jitar tashin hankali.
Bayanin haka ya fito ne a cikin takardar manema labarai dauke da sa hannun shugaban MSSN na yankin, Malam Shafi’i Jume, inda ta ce daliban na matukar fuskantar koma baya ta yawan kulle makarantun yankin, a duk lokacin da aka samu matsalar tsaro.
- Kudancin Kaduna: CAN da SOKAPU sun kaurace wa taron zaman lafiya
- Babu wanda rikicin Kudancin Kaduna bai taba ba – Janar Agwai
“Babban abin bakin ciki shi ne yadda dalibai da malamai da sauran ma’aikata ke jin tsoron zuwa aiki saboda matsalar tsaro, duk da manyan makarantun da ke yankin da suka hada da Kwalejin Ilimi da Kwalejin Aikin Jinya da reshen Jami’ar Jihar Kaduna,” inji sanarwar.
Sannan ya ce rashin isassun jami’an tsaro a yankunan da wasu makarantun suke ne ya sa mafi yawan masallatan da ke makarantun aka kona su, inda ta ba da misali da masallacin Kwalejin Ilimi na Kafanchan da Kwalejin Gwamnati (GCK) da ke Kagoro a Karamar Hukumar Kaura da Sakandaren Gwamnati (GSS) da ke Kafanchan.
Bayan jinjina wa Gwamnan Jihar, Nasir Ahmad El-Rufai kan kokarinsa na samar da tsaro a yankin, kungiyar ta mika kokon bara gare shi kan ya sanya sunan marigayi Sarkin Jama’a na 10, Alhaji Isa Muhammad Sani ga Kwalejin Ilimi ta Jihar Kaduna da ke garin Kafanchan.