Gwamnatin Ukraine ta roki Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA da ta haramta wa kasar Iran shiga gasar Kofin Duniya da za ta gudanar a Qatar.
Hukumar Kwallon Kafar Ukraine ce dai ta gabatar da wannan bukata dangane da babbar gasar tamaular da za a fara ranar 21 ga watan Nuwamba a kuma karkare a watan gobe.
- Ilimin yara mata: Kaduna ta tura malamai 2,000 zuwa makarantu 155
- Buhari ya sauka a London domin ganin likita
Bayan wani zama da kwamitin gudanarwa na Hukumar Kwallon Kafar Ukraine ya gudanar ne kasar ta aike wa FIFA bukatar kunshe a wata sanarwa.
Hukumar ta Ukraine dai ta zargi Iran da bai wa Rasha makamai don taimakawa a mamayar da Moscow ke yi wa kasar.
Rokon ya zo kwanaki kadan bayan da Shugaban kungiyar Shakhtar Donetsk Sergei Palkin ya yi kira da a cire Iran, a kuma bai wa Ukraine din damar maye gurbinta a gasar ta bana.
Ukraine na sahun kasashen da suka rasa gurbi a gasar Kofin Duniyar wadda a wannan karon za ta gudana a Gabas ta Tsakiya.
Ita kuwa Iran wadda ta samu gurbin ta ke fuskantar barazanar gaza zuwa gasar musamman bayan zarge-zargen da ke nuna hannunta a taimakon Rasha.