Masu ruwa da tsaki kan sake fasalin karatun Tsangaya a Jihar Borno sun bukaci gwamnati ta kama tare da sanya yara masu gararamba a kan tituna a makarantun kwana na musamman.
Sun kuma ba da shawarar wajabta wa iyayen da ’ya’yansu ke zuwa Maiduguri karatun allo daga sassan jihar su rika kai musu kayan abinci.
A taron kwana biyu da suka gudanar a Maiduguri, sun ba da shawarar a kafa cibiyar makarantun tsangaya ta zamani ta a kowacce daga mazabun Sanatoci uku a matsayin gwaji a jihar.
Mahalarta taron sun kuma nemi a haramta tura yara ’yan kasa da shekara 12 karatun allo daga wasu garuruwan jihar zuwa Maiduguri.
- ’Yan Kalare: ‘Da haɗin kan jama’a za mu magance rashin tsaro’
- Yadda sojoji suka kashe ’yan ta’adda 481 suka kama 741 a wata guda
Kazalika sun nemi gwamnati ta ɗauki matakan hana kwararowar almajirai daga jihohi da ƙasashe maƙwabta, tare da tallafa wa makarantun tsangaya da malamansu a jihar.
Sun jaddada muhimmacnin gaggauta kafa wata rundunar hadin gwiwa da za ta kunshi hukumar makarantun tsangaya da Islamiyya da sauran hukumomin tabbatar da doka tare da ba su ikon aiwatar da wadannan matakai.
Hakazalika, duk motocin da ke shigowa Maiduguri ya kamata a tantance su da nufin kama abubuwan laifi, musamman matasa marasa aikin yi.
Sanarwa bayan taron da shugaban hukumar makarantun tsangaya da Islamiyya na jihar, Khalifa Ali A. Abulfatihi, ya sanya wa hannu ta ce ya kamata a koyar da yaran da ba sa zuwa tsangaya ko makarantun firamare, a ba su horo kan sana’o’i domin kawar da su daga kan tituna.
Sannan ya nemi bai wa hukumar ikon ci gaba da aikin rijistar makarantun tsangaya da Islamiyya da nufin sabunta bayanan dalibai da malamai kafin watan Maris na shekarar 2025.
Sanarwar ta ce gwamnati ta bullo da tsarin da ya dace na shigo da dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da ’yan siyasa da sarakunan gargajiya cikin ayyukan tallafa wa makarantun tsangaya da malamansu tare da jaddada bukatar tallafa wa duk shirye-shiryen tsangaya a jihar.