An yi kira ga direbobin manyan motoci da ke safarar dabbobi da kayan abinci daga jihohi Arewa zuwa Kudancin kasar nan su kauce wa daukar fasinjoji a motocinsu.
Wannan kira ya fito ne daga bakin Shugaban Kngiyar Masu Safarar Kayan Abinci da Dabbobi ta Kasa, Kwamared Mohammed Tahir, a zantawarsa da manema labarai a Kaduna.
- Ambaliyar ruwa: Pakistan na fuskantar barazana a bangaren ilimi
- ISWAP na shirin kaddamar da hari a Zamfara —Gwamnati
Ya ce makasudin yin taronsu a Kaduna ya biyo bayan damuwa da yadda wasu direbobi ke daukar mutane daga Arewa zuwa Kudu ba bisa ka’ida ba.
Ya ce kungiyar ta fito da dokar haramta daukar mutane a cikin motocin kaya zuwa Kudancin Najeriya, musamman zuwa jihohin Legas da Ribas da sauran jihohin Kudu da Yammacin kasar nan, domin kare mutuncin ’yan Arewa da kuma kasa baki daya.
“Akwai abubuwa da yawa da suke faruwa a kan dakon mutane a kan kaya.
An yi babbar mota ce saboda daukar kaya ba saboda fasinja ba amma saboda rashin sanin ciwon kai da rashin mutunta kai da rashin mutunta al’ummar Arewa, sai ka ga an kwaso mutane 30 zuwa 50 a motar kaya; inda karshenta idan aka yi hadari, sai ka ga mutane sun kakkarye ko wasu sun mutu kuma ga shi ba su da wata takarda da za ta nuna inda suka fito.
“Muna shan wahala wajen bibiyar irin wadannan abubuwa. Sannan jami’an tsaro na wahala wajen gano ’yan uwan irin wadannan mutane.
Wannan ya sa muka ce duk motar da ta dauki kaya a tabbatar kayan ne aka kai amma ban da daukar fasinja a tirela.
“Idan fasinja ne, yana son zuwa wani wuri, ya je tashar mota ya biya kudi, ya je inda za shi babu wanda ya hana shi.
“Kuma ba mu da hurumin da za mu hana shi hawa motar fasinja.
“Amma motar da aka dauko hayarta don daukar kayanmu, kamar shanu da awaki da kayan buhu don a kai Kudu, muna bukatar direban ya kauce wa daukar mutane,” in ji shi.
Ya kara da cewa, “Ana zubar da mutuncin Hausawa da Fulani da mutuncin ’yan Arewa da Najeriya baki daya.
“Misali, kwanan nan motoci biyu suka kwashi mutum 168 da babura 39, alhalin an dauki motar ce a kan ta kai shanu Jihar Legas.
“A daya motar, an sa shanu 34, daya kuma shanu 35 amma kuma suka debi wadannan mutane, har ’yan Amotekun suka kama su a garin Akure, bisa zargin ’yan ta’adda ne.
“Wannan zubar da mutuncin mutane ne kuma zubar da mutuncin kasa ne, a ce mota biyu sun kwashi mutum 168.
“Idan aka dauka aka sa a shafukan sada zumunta, ai zubar da mutuncin kasa ne. Shi ya sa aka sa dokar,” inji shi.
Ya bayyana cewa mutane da dabbobi da yawa ne ke rasa rayukansu idan aka yi hadari a irin wannan yanayi.
Shugaban ya kuma ce sun fito da webil domin magance matsalar safara da satar shanu, ta inda duk motar da ke daukar kaya dole ne a ba ta webil da zai nuna daga inda ta fito kuma wa ke da kayan, sannan wace kasuwa za a kai kayan?