Kungiyar Tsofaffin gwamnoni ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su kauce wa duk wani abu da zai raba kansu da kasar nan.
Shugaban kungiyar, kuma Tsohon gwamnan jihar Neja, Dakta Mu’azu Babangida Aliyu da sakataren kungiyar, Farfesa Tunde Esan suka fitar da sanarwa, a Abuja.
- Ya kamata idan za a raba kasar nan a raba ta cikin mutunci
- Abinda ya sa kabilar Ibo ke boren raba kasa – Sanata Hanga
Takardar na kunshe da sanarwar kamar haka: “Wannan zagayowar ranar samun ‘yancin kai ta musamman na mana tuni da tarihin kasar nan na musamman.
“Yawan al’umma da Allah ya yi wa Najeriya nuni ne na albarka da aka saka a farfajiyar kasar.
“Muna kira ga ‘yan Najeriya da su cigaba da ba kasa muhimmanci.
“Kungiyar hadin kai ta tsofaffin gwamnoni tsaye take kan hadin kan kasar nan da zai cigaba da samar da adalci da sanin yakamata ga mutane.
“Cigaban kasa ya ta’allaka ne kan yawan al’ummar da ake da su. Kasashe kadan suke da irin damar da muke da ita
“Kar mu yadda yawan mu ya ki yi mana amfani, mu yi amfani da wannan damar mu taimaki kanmu da sauran bakaken fata.
“Ya kamata a bar yunkurin ganin kasar nan ta rarrabu ta fannin kiyayyar kabilanci da yankin kasa. Hakkin mu ne samar da zaman lafiya ga ‘yayan mu da jikokinmu masu zuwa,” inji Kungiyar.
Wannan kiran dai na zuwa ne a daidai lokacin da kabilun da ke yankin kasar nan ke barazanar ballewa daga.