✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A garin yawon Sallah ruwa ya cinye yarinya

A daidai lokacin da ake tsaka da farin cikin bukukuwan Sallah, mutanen garin Birnin Yero ta jihar Zamfara kuwa sun wayi gari ne da alhinin…

A daidai lokacin da ake tsaka da farin cikin bukukuwan Sallah, mutanen garin Birnin Yero ta jihar Zamfara kuwa sun wayi gari ne da alhinin rashin ’yarsu mai suna Maryam Hashim, ’yar shekara 12; wadda ta rasa ranta sakamakon faɗawa kogin da ta yi a lokacin da take kan hanyarta ta zuwa gida daga yawon Sallah.
Malam Sa’idu Hashim Gidan Gobirawa, wa ne ga marigayiyar. Ya shaida wa Aminiya cewa: “Da yammacin Alhamis ne kawarta ta nemi su tafi yawon Sallah a wani ƙauye da ake kira Dole, amma sai ta faɗa mata cewa yamma ta yi, don haka su bari in garin Allah ya waye. Sai ƙawar ta nuna mata cewa ai ita a washegarin mahaifiyarta za ta daka mata dawo ta je talla, don haka in an bari a goben ma sai dai su tafi da yamma. Hakan ce ta sanya suka ɗunguma su biyu, suka nufi uguwar Dole. Ko da suka je bakin rafi sai suka ga mutane na bin wani ratse a gulbin, ta haka su ma suka ratsa suka wuce domin ita Maryam ba saba zuwa wurin ta yi ba ko da rana ido na ganin ido.”
Ya ci gaba da bayanin cewa: “A daidai lokacin da suka dawo daga yawon Sallar ne, sun nufo bakin rafin a lokacin dare ya fara yi, don an daɗe da idar da Sallar Magariba. Ko da suka zo gaɓar ruwan sai suka kasa gane inda suka bi suka ratsa da farko, abin da ya sanya su shawarar komawa da baya amma sai suka yi gudun kada a yi musu faɗa a gida. A hakan ne suka daure suka riƙe hannun junansu, suka ratsa cikin gulbin.
“kawar marigayiyar wadda ta tsira da ranta, ta ce sai kawai ta ga ruwa na tafiya da ita. A haka ya kai ta bakin gaɓa ta fita, daga nan ne ta lura ba ta ga ’yar uwarta ba. Nan ta iske wani mutum wanda ya shiga ruwan ya yi ta lalube ba tare da ya gan ta ba. Daga nan ne ya rako ƙawar tata gida.” Inji shi.
Yayan Marigayiyar ya ƙara da cewa a daren da labarin ya riske su, sun ɗebi jama’a aka baza neman ta cikin rafin amma har dare ya ratsa ba su gano ta ba. A haka suka haƙura gari ya waye, suka ci gaba da nema har sai da suka yini guda suna nema amma Allah bai sa sun gano ta ba. Sai bayan kwana daya, aka kira su a waya, aka sanar da su cewa an gano gawarta. “Nan muka je muka iske ta, muka yi mata sutura. Babu abin da za mu ce sai dai mu gode wa Allah. Mun iske ta cikin kyakkyawan yanayi, duk da cewa a ƙugurmin daji muka gano ta.” Inji shi.Shugaban makarantar Makarantar Hifzul kur’an wata allim da ke Birnin Yero, a karamar Hukumar Shinkafi, Malam Ibrahim Umar, ya bayyana Maryam a matsayin ɗaliba mai haƙuri da hazaƙa tare da ladabi da biyayya. Kana ya miƙa ta’aziyyarsa a madadin ɗaukacin malaman makarantar da ’yan uwanta ɗalibai ga iyayenta da ’yan uwanta baki ɗaya.