✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A farkon 2023 za mu fara tunkudo iskar Gas zuwa Kaduna da Kano – NNPC

NNPP ya ce yana da kwarin gwiwar kammala aikin a farkon 2023

Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) ya ce yana da kwarin gwiwar fara tunkudo iskar gas daga Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano (AKK) nan da farkon shekarar 2023 mai zuwa.

Shugaban kamfanin, Mele Kyari ne ya bayyana hakan, lokacin da mambobin hukumar gudanarwar kamfanin suka ziyarci daya daga cikin yankunan da lamarin ya shafa a Abaji, Babban Birnin Tarayya Abuja, ranar Alhamis.

Ya ce yana da kwarin gwiwar cewa yunkurin da suke da shi na kammala aikin a cikin wata ukun farkon shekarar zai tabbata.

Malam Mele Kyari ya ce aikin, da zarar an kammala shi, zai bunkasa samar da makamashi da wutar lantarki, ya samar da ayyukan yi sannan ya rage yawan dogaro da itace wajen yin girki.

Ya ce aikin wani muhimmin yunkuri ne da za a jima ana tuna gwamnati mai ci da shi, yana mai cewa lokaci ya yi da Najeriya za ta fara cin gajiyar albarkacin gas din da take da shi fiye da kowacce kasa a nahiyar Afirka.

Ita kuwa a nata jawabin, shugabar Hukumar Gudanarwar NNPC, Margret Okadigbo, ta ce la’akari da irin aikin da aka shimfida ya zuwa yanzu, akwai yiwuwar a fara tunkuda gas din nan da farkon shekarar mai zuwa.

Shi ma shugaban kamfanin Oilserv da ke aikin shimfida bututan gas din, Mista Emeka Okwuosa, ya tabbatar da aniyar kamfaninsa wajen kammala aikin kamar yadda aka tsara.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne  dai ya kaddamar da aikin shimfida bututan masu nisan kilomita 614 a shekarar 2020 don bunkasa amfani da gas a matsayin makamashi da kuma fargado da masana’antu.