✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A fara duban watan Karamar Sallah ranar Alhamis —Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi ya bukaci Musulmi cewa su fara neman jinjirin watan Karamar Sallar 2023 daga ranar Alhamis, 20 ga watan Afrilu

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci al’ummar Musulmin Najeriya su fara duban jaririn watan Shawwal a ranar Alhamis domin yin Karamar Sallah.

Sarkin Musulmi wanda shi ne Shugaban Majalisar Koli kan Harkokin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ya ba da sanarwar ce ta hannun Daraktan Gudanarwar Majalisar, Zubairu Haruna Usman-Ugwu.

Malamai sun bayyana cewa ganin sabon watan Shawwal shi ne babbar alamar karewar watan Ramadan, amma idan ba a gani ba sai a cike azumin Ramadan kwana 30; daga nan sai a yi karamar Sallah, ko da watan bai fito ba.

Ranar Alhamis za ta kasance 29 ga watan Ramadan 1444 Hijiriyya da muke ciki, wanda shi ne ranar da ake fara duban jinjirin watan Shawwal.

“Idan Musulmi sun ga watan aka kuma tabbatar, Mai Alfarma Sarkin Musulmi zai ayyana Juma’a 21 ga watan Afrilu, 2023 a matsayin 1 ga watan Shawwal, wato ranar Karamar Sallah.

“Amma idan ba a gani ba, sallah za ta kasance washegari 22 ga wata,” in ji sanarwar.

Ya bukaci Musulmi da sauran shugabannin al’ummar Musulmi da cewa da zarar an tabbatar da ganin wata a yankunansu, su hanzarta sanar da Kwamitin Gwanin Wata na Kasa.

Sarkin Musulmin ya kuma jaddada wajibcin fitar da Zakatul Fidr a kan kowane Musulmi, wanda ake ba wa matalauta kafin a yi Sallar Idin karamar Sallah.

A karshe ya yi wa al’ummar Musulmin duniya murnan zuwan sallar tare da addu’ar Allah Ya yi musu tsawon kwana.

Ya kuma bukaci ’yan Najeriya da su dukufa wajen addu’o’i a kwanakin da suka rage na watan Ramadan domin samun aminci da ingantuwa rayuwa a kasar.