Assalamu Alaikum, Editan Aminiya ina mika gaisuwata ga kamfanin jaridun Aminiya, watau Daily Trust da Weekly Trust da Sunday Trust da sauransu. Tare da fatan alheri ga daukacin ma’aikatanku.
Ina kira ga shugabannin Arewa tun daga kan shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsofaffi da kuma sababbin ministocin da ake jiran a nada da gwamnoni da manyan mutane masu fada a ji a Arewa mazansu da matansu, su taimaka don a farfado mana da kamfanin buga jaridun Gaskiya Ta Fi Kwabo da New Nigerian. A gaskiya Arewa mun yi rashin wannan kamfani mai muhimmanci da marigayi Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ya gina. Allah Ya ba da iko, amin.
Daga Alfa Adamu (Adamu Alheri) mai sayar da jaridu a Lakwaja, Jihar Kogi 08067075867