✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A dauki mataki kan kisan matafiya a Jos — FOMWAN

Kungiyar ta ce hukunta wanda suka aikata kisan zai zama izina ga na baya.

Kungiyar Tarayyar Mata Muslim ta Najeriya (FOMWAN), ta bayyana damuwarta kan kisan da aka yi wa matafiya 27 da safiyar ranar Asabar a Jos, babban birnin Jihar Filato.

Kungiyar ta bayyana damuwarta cikin sanarwar da Shugabanta ta Kasa, Hajiya Halimah Jibril ta fitar ranar Litinin a Abuja, tana mai bayyana lamarin a matsayin abun kyama.

  1. Ba ni da sha’awar zama Shugaban Kasa — Sarki Sanusi
  2. Mutum fiye da 1,300 sun mutu a girgizar kasar Haiti

Da ta ke Allah-wadai da lamarin, FOMWAN ta bukaci gwamnati da ta gudanar da bincike cikin hikima don gurfanar da wanda suka aikata laifin.

 “FOMWAN ta yi bakin ciki da wannan mummunan laifi da aka aikata, don haka muna tuni akan a gurfanar tare da hukunta wanda suka aikata laifin don zama izina ga wanda suka da tunani irin wannan.

“Za mu iya tuna cewar akwai wani lamari da ya faru makamancin wannan a Filato inda aka kashe mutane yayin da suke sallar idi sannan aka kone gawarsu.

“Haka kuma labarin kisan da aka yi wa Janar Alkali a 2018 har yanzu na nan a ranmu,” a cewarta.

Kazalika, ta shawarci gwamnati kan daukar matakin da ya dace saboda gujewa faruwar irin wannan ta’addanci ba wai a iya Filato ba, a ko ina a fadin Najeriya.

Ta ce “A matsayinmu na musulmai mun san darajar ran kowane dan Adam, don haka babu wani mutum da ya ke da ikon daukar rayuwar wani face Allah Subhanahu Wata’ala.

Hajiya Halimah ta shawarci gwamnati da sauran jami’an tsaro da su fahimci yanayin da ake ciki wajen yanke hukuncin da ya dace don gujewa harzuka wasu.

“Muna rokon mutane da su zauna lafiya tare da gujewa daukar doka a hannunsu.

“FOMWAN tana jajanta wa iyalai da makusantan wadanda harin ya shafa.

“Muna addu’ar samun rahama ga wanda suka rasu sannan muna addu’ar samun zaman lafiya a kasarmu,” a cewarta.

Aminiya ta ruwaito cewa, matafiyan da aka kashe na kan hanyar su ta komawa Jihar Ondo bayan sun halarci taron bikin sabuwar shekarar Musulunci a Jihar Bauchi.