✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A daina sanya ni a kowane irin wasa – Messi

Shahararren dan kwallon FC Barcelona na Sifen Lionel Messi ya koka a kan yadda kulob din yake yawan sanya shi buga kowane irin wasa.  Ya…

Shahararren dan kwallon FC Barcelona na Sifen Lionel Messi ya koka a kan yadda kulob din yake yawan sanya shi buga kowane irin wasa.  Ya ce yakamata a rika mutunta shi kamar yadda kulob din Real Madrid yake mutunta takwaransa Cristiano Ronaldo ta hanyar ba shi hutu a wasannin da ba su da zafi.

Lionel Messi ya bayyana haka ne a lokacin da yake hira da kafar watsa labaran wasanni ta Diario Gol a Sifen a ranar Talatar da ta wuce,  ya ce ba kowane irin wasa ne yakamata ya rika yi a kowane lokaci ba.  “Akwai wasanni marasa zafi da ba lallai sai na buga su ba, kamar yadda akwai wasannin da yakamata a ce na buga”, inji Messi.

Kulob din Madrid dai yana ba Ronaldo hutu inda kawo yanzu ya huta a wasanni da dama a gasar La-Liga ta bana, amma Messi ba wasan da bai buga wa kulob din a bana ba.

Rahotanni sun nuna kawo yanzu Messi ya yi wa Barcelona wasanni 39 ne a kakar wasa ta bana, da hakan ta sa ya taimaki kulob din wajen kasancewa na daya a Gasar La-Liga ta Sifen.