✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A cika alkawarin da aka yi game da Ajaokuta

Lokacin dadin baki ya wuce - kawai a yi aiki

Kamfanin Karafa na Ajaokuta, wanda aka kafa a 1979 aka kuma kammala kashi 90 cikin 100 na aikin gina shi tun a shekarar 1983, zai iya taka muhimmiyar rawa a yunkurin fadada tattalin arzikin kasa da bunkasa masana’antu da samar da ayyukan yi da samar da kudaden musaya.

Sai dai, duk da fahimtar haka, gwamnatocin da suka mulki kasar nan dadin baki kawai suka rika yi suna alkawarin kammala kamfanin, yayin da ma’aikatan gwamnati marasa kishin kasa ke ci gaba da hada baki da kamfanonin kasashen waje suna sace kayan aikin da ke wurin, suna hana Najeriya cin gajiyar amfanin da za a iya samu daga gare shi.

Kowace shekara, ana kebe kudi don kamfanin na karafa, amma har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.

Wani rahoto na baya-bayan nan da ya nuna cewa an narkar da kusan Naira biliyan 20 a kamfanin a cikin shekara shida da suka gabata, ba tare da an samu wani amfani ba, wani abin bakin ciki ne game da rikon sakainar kashi da gwamnati ta yi wa ci gaban kasa.

Duk da alkawarin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi lokacin yakin neman zabe a 2015 a Lokoja babban birnin Jihar Kogi, cewa zai bayar da fifiko ga farfado da kamfanin, shekaru shida ke nan na mulkinsa – ma’ana, saura shekara biyu kacal wa’adinsa na biyu yak are – amma babu wani abu da aka yi wanda a zahiri ke nuna cewa zai cika wannan alkawari.

Saboda fa’idar tattalin arzikin da za a iya samu daga Ajaokuta, kamfanonin kasashen waje sun nuna sha’awarsu, amma sabida halin ko-in-kula da gwamnati ke nunawa, wadannan kamfanonin ko dai sun yagi abin da za su yaga ko kuma cikin takaici sun juya wa lamarin baya.

Na farko dai shi ne kamfanin TYAZHPROMEDPORT (TPE) na Rasha, wanda ya fara aikin a 1979, sannan kamfanin SOLGAS ENERGY Limited na Amurka, sai kamfanin Global Infrastructure Nigeria Limited (GINL), da kamfanin REPROM Company Nigeria Limited, wanda ya yi bincike kan kamfanin, kafin gwamnati ta mayar da shi karkashin shugabancin wucin-gadi.

Babu yunkuri daya daga cikin wadannan da ya kai ga biyan bukata.

Wani bincike mai zurfi da masana a fannin suka yi ya nuna cewa, idan gwamnati ta kuduri aniyar farfado da Ajaokuta, za a iya fara aiki a tara daga cikin rukunoninsa a cikin wata shida.

Ta hanyar hada gwiwa da Kamfanin Hakar Tama da Mai na Najeriya da ke Itakpe, wanda zai samar da narkakken karfe, kamfanin Ajaokuta ka iya samar da dubban ayyuka da alkinta biliyoyin dalolin da ake kashewa wajen shigo da karafa a kowace shekara don ayyukan gine-gine, da aikin shimfida layin dogo da bangaren man fetur da fasahar sadarwa (ICT), har ma da tsaro da kera makamai.

Abubuwan da suka hana cimma wannan buri sun hada da cin hanci da rashawa da sarkakiyar shari’a mara kan gado, da gazawa ta fuskar gudanarwa.

Gwamnati ta gaza tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro wajen magance wadannan matsaloli masu tayar da hankali, lamarin da ya sa Najeriya ta yi nusan duk da karfin da ta taskace, a maimakon ta tattalin arzikinta ya bunkasa ta hanyar bunkasa karafa.

Ministan Ma’adanai da Karafa, Olamilekan Adegbite, ya ce gwamnati ta kulla wata yarjejeniya ta hadin gwiwa tsakanin gwamnati da ’yan kasuwa da was kamfanonin Rasha kan farfado da kamfanin.

Idan aka yi la’akari da Shirin na asali, wanda aka fara a shekarar 2019, ya kamata a ce kwararrun Rasha su ziyarci Ajaokuta don tantance halin da kamfanin ke ciki, kuma zuwa sulusin karshe na 2022, ya kamata a ce Buhari ya kaddamar da masana’antar ta fara samar da karafa.

Sai dai an ce wannan jadawali ya ci karo da cikas sakamakon bullar annobar COVID-19.

Samar da kudin da za yi wannan hadin gwiwa bai kamata ya yi wahala ba, saboda dimbin ribar da aikin zai samar.

Muna kira ga gwamnati da ta matsa daga zancen fatar baka game da bunkasa Ajaokuta ta dauki kwakkwaran mataki don ganin an fara fitar da karafa daga masana’antar.

Dole ne ta tabbatar an aiwatar da yarjejeniyar da aka yi yanzu tare da masu saka hannun jari na Rasha.

Idan gwamnati ta tsaya tsayin daka don kammala wannan aikin, Kamfanin Karafa na Ajaokuta zai iya samar da dimbin karafan da ake bukata don aikin samar da wutar lantarki a Mambilla wanda ’yan China ke gudanarwa.

Bisa ga dukkan alamu, Gwamnatin Buhari na da dama da sukunin farfado da Ajaokuta.

Don haka, a maimakon a yi gta surutu, kawai wannan gwamnatin ta yi aiki – ta farfado da wannan gagarumin kamfanin na karafa.