✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jirgin kasa ya yi awon gaba da motar ma’aikata a Legas

Jirgin kasan ya yi awon gaba da motar yayin da ta ke shirin tsallaka titin dogo.

Akalla ma’aikatan gwamnatin Jihar Legas biyu ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon awon gaba da wani jirgin kasa ya yi da wata motar bas a hanyar a yankin Sogunle a jihar.

An gano cewa wata motar BRT da ke kai ma’aikatan gwamnatin jihar zuwa aiki, ta so tsallaka layin dogo ne a lokacin da jirgin da ke tafiya ya makale.

Kakakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Ibrahim Farinloye ya ce “An gano gawarwakin ma’aikatan mata biyu na gwamnatin jihar, an kuma kwashe wadanda suka jikkata da dama.

“Bas din ma’aikatan gwamnatin jihar na kokarin tsallaka titin jirgin kasa a Sogunle yayin da jirgin da ya taso daga Abeokuta zuwa Legas, ya makale,” inji shi.

Tuni aka dauki wadanda suka jikkata zuwa asibiti don ba su kulawar da ta dace.