Gare ki uwar ’ya’ya (Kunya da amana)
Daga Salihu Makera
Assalamu alaikum warahmatullah.
Kamar yadda muka sani ginin al’umma yana farowa ne daga gida, kuma uwa ita ce ruhin kowane gida, idan ta kasance tagari, sai gidan ya kasance nagari. A ci gaba da darasinmu yau za mu duba wasu kyawawan halaye ne da ake so uwar ’ya’ya ta siffantu da su kuma ta dora ’ya’yanta a kansu. Wadannan halaye su ne KUNYA da AMANA.
Kunya:
K |
unya kyakkyawar dabi’a ce da take sa mutum ya bar abubuwan ki, take hana shi tauye hakkokin jama’a. Ba rashin magana ko sanyi-sanyi a tsakanin mutane ba ne kunya.
Kunya siffa ce daga cikin siffofin Annabi (SAW), ta yadda aka siffanta shi (SAW) da cewa ya fi amarya kunya a dakinta a daren farko, amma a tare da haka (SAW) ba ya jin tsoron zargin mai zargi wajen yin abin da yake daidai. Kunya yanki ne na imani kamar yadda ya zo a cikin Hadisi, don haka akwai alaka sosai a tsakanin rashin kunya da aikata zunubi. Duk lokacin da kunya ta yi karanci aikata zunubi da sabo za su yawaita, duk lokacin da kunya ta karu, sai aikata zunubi da sabo su ragu. Kan haka ne Allah Madaukaki Yake cewa: “Ashe (mutum) bai sani ba (duk abin da ya yi) cewa lallai Allah Yana gani.” (Alak:14).
Wajibi ne uwa ta koya wa ’ya’yanta jin kunyar Allah ta hanyar nuna girman Allah gare su. Ta koya musu cewa su rika jin kunyar kada Allah Ya gan su a inda ba Ya so, ko Ya gan su suna aikata sabo suna keta umarninSa suna aikata hane-hanenSa. Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ku ji kunyar Allah iyakar jin kunya.” Sai (sahabbai) suka ce: “Lallai mu muna jin kunya ya Manzon Allah! Sai ya ce: “Ba wannan ba, amma wanda ya ji kunyar Allah iyakar jin kunya, sai ya kiyaye kai da abin da ya tsare (haddace) da ciki da abin da ke kewaye da shi, kuma ya rika tuna mutuwa da bala’i. Kuma wanda yake nufin Lahira, to, ya bar kawar duniya. Wanda ya aikata haka hakika ya ji kunyar Allah matukar jin kunyarSa.” (Tirmizi da Ahmad).
A wannan Hadisi za mu ga Annabi (SAW) yana nuna mu kiyaye iliminmu daga abin da zai kai mu ga hallaka haka mu kiyaye cikinmu daga cin abin da zai kai mu ga hallaka haka sauran gabbanmu. Kuma mu rika tuna mutuwa, wannan zai sa mu guji duk abin da zai ja mu zuwa ga aikata sabo ko zunubi kuma ya ce mu rika tuna aukuwar bala’i. Sannan ya ce mu guji kawar duniya matukar muna son mu ji dadi a Lahira.
Ya ke uwar ’ya’ya! Shin kina kiyaye wadannan abubuwa kuma kina koyar da ’ya’yanki don su guje musu tare da aikata abubuwan da za su sa su hadu da Allah lami lafiya a Lahira ko kuwa kawar duniya da kyale-kyalenta ne kika fi dora su a kai? Annabi (SAW) ya yi gargadi sosai kan aikata abin da mutum ya ga dama da kuma nuna rashin kunya inda yake cewa: “Yana daga cikin abubuwan da mutane suka riska daga cikin kalaman annabawan farko cewa, idan ba ka jin kunya ka aikata abin da ka ga dama!” (Bukhari), kuma (SAW) ya ce: “Kunya ba ta zuwa da komai sai alheri.” (Muttafakun).
Alamun kunya ga mutum a ga yana son Allah da kiyaye dokokinSa da girmama Shi da ganin ni’imar Allah da gazawar shi bawan wajen nuna godiya a kanta da jin tsoro da kyautata fata da yi wa kai hisabi da zama da mutanen kirki masu biyayya ga Allah.
Idan ke uwa ba ki da wadannan halaye, kuma ba ki dora ’ya’yanki a kansu ba, to ki sauya salo matukar kina son haduwa da Allah lami lafiya.
Amana
Amana tana daga cikin kyawawan siffofin muminai masu gaskiyar imani. Amana tana hana mutum aikata ha’inci da tauye hakkokin jama’a. Allah Ya yabi masu amana a wurare da dama cikin Alkur’ani Mai girma, daya daga ciki Yana cewa: “(Muminan da suka samu babban rabo su ne) Wadanda suke su game da amanoninsu da alkawarinsu masu kiyayewa ne.” (Muminun: 8).
Ya ke uwar ’ya’ya! Ki sani babbar amanar da ake so ki sauke kuma ki koyar da ’ya’yanki ita ce amanar takalifiyya da shari’a ta dora wa kowane mukallafi na kadaita Allah da bauta maSa da yin duk wani aiki da shari’a ta dora wa dan Adam. Wannan amana ce sammai da kasa da duwatsu suka jin tsoron dauka amma mutum ya dauka.
Ibn Abbas (RA) ya ce: “Amana ita ce farillan da aka dora wa dan Adam.” Abul Aliya kuma ya ce: “Ita ce abin da aka umarce su da abin da aka hane su.” Don haka Sallah amana ce, azumi amana ne, Hajji amana ne, haka sauran umarce-umarce da hane-hane.
Ki koya wa ’ya’yanki tsare amanar gabbansu, ido da kunne da harshe da hannuwa da kafafu da al’aura, kada a sarrafa su a inda ba su dace ba. Haka ki koyar da ’ya’yanki tsare amanar dukiya da tsare amanar aikin da aka ba su da tsare amanar sirri da mutuncin mutane. Kusan cikin komai akwai amana da ta wajaba ki tsare kuma ki koya wa ’ya’yanki su tsare su.
Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai Allah Yana umartarku da ku mayar da amanoni zuwa ga masu su.” (Nisa’i: 58). Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ka bayar da amana ga wanda ya ba ka amana, kuma kada ka ha’inci wanda ya ha’ince ka.” (Tirmizi da Abu Dawud)
Duk mai cin amana yana ha’intar Allah da ManzonSa (SAW) ne kamar yadda Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Kada ku ha’inci Allah da Manzon (Allah) kuma ku ha’inci amanoninku alhali kuna sane.” (Al-Anfal:27). Kuma Manzon Allah (SAW) ya sanya ha’inci a cikin siffofin munafukai inda ya ce: “Alamun munafuki uku ne: idan ya yi magana ya yi karya, idan ya yi alkawari ya saba, idan aka ba shi amana ya yi ha’inci.” (Muttafakun)
Annabi (SAW) ya yi magana kan amana sai sahabbai suka nemi ya yi bayani kan yadda amana za ta gushe a tsakanin al’umma sai ya ce: “Mutum zai yi barci sai a cire amana daga zuciyarsa, sai mutane su wayi gari suna kasuwanci amma dayansu bai iya tsare amana.” (Muttafakun).
Wannan shi ne halin da muka tsinci kanmu a ciki yau ya ke uwar ’ya’ya! Mun watsar da rikon amana mun mayar da rayuwarmu kamar ta dabbobi. Allah Ya tsare mana imaninmu.