✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: Tsohon Babban Hafsan Sojin Sama ne zai yi wa APC takarar Gwamna a Bauchi

Sadiq ya doke sauran ’yam takarar inda ya samu nasarar

Tsohon Babban Hafsan Sojojin Sama na Najeriya, Iya Marshal Sadiq Abubakar (mai ritaya), ya lashe zaben fid da gwaninn kujerar Gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Bauchi.

Yanzu dai Sadiq ne dan takarar da zai wakilci jam’iyyar a zaben gwamna mai gabatowa a 2023.

Ya sami nasarar lashe zaben ne bayan ya samu kuri’a 370, inda ya kayar da Sanata Halliru Dauda Jika, Sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, wanda ya samu kuri’u 278, sai kuma mafi karancin shekaru a cikin ’yan takarar, Nura Manu Soro wanda ya samu kuri’u 269.

Kazalika, Dokta Musa Babayo ya samu kuri’a 70, Farouk Mustafa ya samu kuri’u 26, Mahmood Maijama’a wanda ya samu kuri’u takwas, Tsohon Ministan Lafiya, Dokta Ali Pate bai samu kuri’a ko guda daya ba.

Da yake bayyana Sadiq a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kwamitin zaben, kuma tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Ali Sa’ad Birnin Kudu, ya ce Sadiq Abubakar ne ya samu kuri’u mafi yawa tare da bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fid da gwani na Gwamna na jam’iyyar.

A jawabinsa na karbar sakamakon zaben, Sadik ya gode wa daliget din da suka zabe shi tare da bayyana nasarar da ya samu a matsayin nasarar jam’iyyar ta samu.