Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi watsi da rade-radin da ke cewa ta fasa amfani da sabon tsarinta na amfani da na’urorin Bvas da IRev, wajen watsa sakamakon zabe kai tsaye ta intanet daga rumfunan da aka kada kuri’a.
Shugaban Sashin Wayar da Kai da Watsa Bayanai na hukumar, Festus Okoye ne ya bayyana haka ranar Juma’a a Abuja.
- Gwamnati ta sake maka Nnamdi Kanu a kotu
- Shugaban FRSC ya taya Sarkin Musulmi murnar cika shekaru 16 a karagar mulki
A cewarsa, rahotannin da wasu kafofin yada labarai ke yadawa cewa hukumar za ta ajiye tsare-tsare don tafka magudi a zabukan 2023, ba gaskiya ba ne.
“Hukumar na kara tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za ta watsa sakamakon zabe tun daga rumfunan da aka jefa kuri’a, kamar yadda aka gani a zabukan gwamnonin jihohin Ekiti da Osun.
“Sannan kamar yadda aka gani, bayan wadannan jihohin ma, da tsarin aka yi amfani a zabukan cike gurbi na mazabu 103, da aka yi.
“Kuma sakamakon har yanzu yana nan a shafin hukumar idan kuka duba.”
Kazalika, ya ce ya kamata al‘umma su yi watsi da jita-jitar, domin ba gudu ba ja da baya kan amfani da sabbin tsare-tsaren a dukkanin zabukan 2023 masu karatowa.