✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: Tinubu ji yake kamar bashi yake bin APC – Rochas Okorocha

Ya ce Tinubun ji yake kamar ba shi takarar biyan bashi ce a wajensa

Tsohon Gwamnan Jihar Imo kuma mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC, Sanata Rochas Okorocha, ya ce yadda Bola Tinubu ke neman takara ta kowace fuska na nuna kamar bashi yake bin jam’iyyar.

Don haka Okorocha ya ja hankalin Tinubu kan cewa kamata ya yi a bai wa bukatun kasa muhimmanci fiye da komai.

Okorocha ya yi wadannan kalamai ne yayin wata tattaunawa da tashar ARISE TV ta yi da shi kwanan nan.

Game da yinkurin da ’yan takarar Shugaban Kasa daga yankin Kudu maso Gabas ke yi na ganin APC ta tsayar dan takara daga kabilar Ibo, Okorocha ya ce duk dai yana girmama Tinubu sosai, amma batun son mulki ya koma Kudu maso Gabas abu ne da yake a zahiri.

“Ina ganin abu ne a zahiri da ya kamata kowa ya sani, ban san abin da ke zuciyar Tinubu ba amma ina girmama shi matuka, sai dai Tinubu ya damu sosai game da burinsa na son zama Shugaban Kasa.

“Saboda a tunaninsa lokaci ya yi da ya kamata a saka masa duba da irin rawar da ya taka wajen kafa APC, wacce tare da wasunmu aka sha gwagwarmayar kafa ta,” inji Okorocha.

Sanatan ya kara da cewa, “Kowa na da dalilin da ya sa ya fito takara. Tinubu ya yi amannar cewa ya kakkafa mutane da daman gaske, don haka yake ganin yanzu ne lokacin da ya dace mutane su kyale shi ya cimma burinsa.”

Ya ci gaba da cewa “Amma abin ya wuce haka saboda batun Najeriya ake yi. Kamata ya yi mu saka kasarmu a gaba sannan bukatunmu su biyo baya,” inji shi.

%d bloggers like this: