Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Dokta Mustapha Inuwa ya ajiye mukaminsa don tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar a zaben 2023.
Sakataren Gwamnatin shi ne mutum na farko da ya bayyana kudurinsa na neman kujerar gwamnan jihar.
- Sojoji sun kama bindigogi 517a Filato da Kaduna
- Aisha Buhari ta gayyaci ’yan takarar shugaban kasa liyafar bude baki
Kazalika, Mai Bai Wa Gwamna Aminu Bello Masari Shawara ta Fuskar Siyasa, Alhaji Kabir Shu’aibu Charanci, shi ma a ya ajiye mukamin.
Yi kuma ya yi murabus ne domin tsayawa takarar kujerar dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Katsina ta Tsakiya.
Dukkansu, su biyun, sun ajiye mukaminsu a ranar Alhamis, 21 ga watan Afrilu, 2022.
Hakan na zuwa ne bayan jam’iyyarsu ta APC ta sanar da kudin takardun takarar shugaban kasa da gwamna da kuma majalisar dokoki ta kasa da ta jihohi a zaben 2023.
A ranar Laraba ne dai uwar jam’iyyar, bayan taron farko na kwamitin gudanarwarta ta sanar da kudaden takardun takarar.
Tuni dai masu rikie da mukaman siyasa da sauran ’yan siyasa masu hankoron shiga zaben 2023 suka fara bayyana manufarsu.
Masu rike da mukaman siyasa daga cikinsu, tuni suka fara ajiye mukamansu domin fusktar abin da suka sa a gaba.