✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: Peter Obi ya zabi Yusuf Baba-Ahmed abokin takara

Kudirin jam'iyyar ba zai cika ba dole sai an hada mutane masu aniya iri daya.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya zabi Dokta Yusuf Baba-Ahmed a matsayin mataimaki wanda za su yi takara tare a zaben 2023.

Obi ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma’a a wajen wani taron jam’iyyar da suka gudanar a Abuja.

A cewar dan takarar, yanzu jam’iyyarsu ta samu wanda ya cancanci zama Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya don tabbatar da tsaron kasa, hadin kai da kuma bunkasarta.

Tsohon gwamnan Jihar Anambran ya ce burin jam’iyyarsu ne ta yi wa Najeriya hidima yadda ya kamata domin inganta ci gabanta.

Ya kara da cewa, kudirin jam’iyyar ba zai cika ba dole sai an hada mutane masu aniya iri daya don cimma manufa.

Sa’ilin da yake gabatar da mataimakin nasa, Obi ya ce, “Bisa girmamawa, ina mai gabatar muku da wani da nakan kira da abokina, kanina, kuma Mataimakin Shugaban Najeriya na gaba da yardar Allah mai suna Sanata Yusuf Baba-Ahmed.

(NAN)