Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban Kasa a zaben 2023 mai zuwa a tutar jam’iyyar APC.
Ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter da sanyin safiyar Litinin.
- NAJERIYA A YAU: Yadda ruwan sha ke neman gagarar talakan Kano, Katsina da Jos
- Za a je zagaye na biyu a zaben Shugaban Faransa
Osinbajo ya ce, “A yau, ina mai kaskantar da kai wajen bayyana aniyata ta tsayawa takarar kujerar Shugaban Kasar Najeriya a tutar jam’iyyar APC ”
Gabanin haka, Mataimakin Shugaban Kasar sai da ya shirya buda-baki ga wasu Gwamnonin APC a gidansa na Fadar Gwamnati a Abuja da yammacin ranar Lahadi.
Wata majiya a Fadar Shugaban Kasa ta ce Farfesa Osinbajon sai da ya tattauna da Gwamnonin a kan kudurin nasa, gabanin ayyanawar ta ranar Litinin.
A cewar majiyar, “A matsayinsa na Shugaban Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa tsawon shekara bakwai, yana da kyakkyawar alaka da Gwamnonin kowacce jam’iyya kuma daga kowane sashe na kasar nan.
“Da yawa daga cikin Gwamnonin kuma mambobi ne ko Daraktoci a wasu hukumomin gwamnati, wadanda Osinbajon yake jagoranta, wanda hakan kuma ya kara dankon dangantaka a tsakanin shi da su,” inji majiyar.
Wata majiyar kuma ta ce Mataimakin Shugaban Kasar ya jinkirta ayyana takarar tasa ce saboda matsayinsa a gwamnati.
Wasu daga cikin Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da na Kaduna, Nasir El-Rufa’i, da na Ogun, Dapo Abiodun da na Imo, Hope Uzodinma da kuma na Legas, Babajide Sanwo-Olu.
A watan da ya gabata ne dai muka baku labarin cewa Osinbajon ya sanar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari aniyar tasa ta neman kujerar Shugabancin Najeriya a 2023.
Ya zuwa yanzu dai, wadanda suka ayyana neman tsayawa takarar sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu da tsohon Gwamnan Imo, Rochas Okorocha da Gwamnonin Jihohin Kogi (Yahaya Bello) da na Ebonyi (David Umahi) da kuma Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.