Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya musanta zargin janye wa takwaransa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar takara.
Wannan na zuwa a yayin da ‘yan watanni suka rage a shiga zaben shugaban kasa a watan Fabrairun badi.
Ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi kungiyar Editocin Najeriya NGE a Jihar Legas.
Kwankwaso ya bayyana cewa idan har zai janye wa Atiku takara, da bai fice daga PDP ba watanni kadan kafin Zaben shugaban kasa.
“Wasu mutane na cewa na janye wa Atiku; me ya sa na bar jam’iyyar? Wadannan su ne matsaloli; ka ga matsalar jam’iyyar ita ce, akwai mutane da yawa da suke ganin sun fi karfin komai.
“A tsarin dimokuradiyya, mutane suna da ‘yancin shiga kowace jam’iyyar siyasa, ba za ku iya zama a can ku fara cewa ina son wannan ba, ko kuma ba ku son wani ba.”
Dan takarar jam’iyyar NNPP, ya ce akidarsa da gogewarsa sun sha bamban da na abokan hamayyarsa wanda ya buga misali da lokacin da yake gwamna a Jihar Kano.