Maidakin dan takarar shugaban kassa na Jam’iyyar APC, Sanata Oluremi Tinubu, ta ce, tana fatan Najeriya ta samu ’yan takarar Shugaban Kasa Kirista da Kirista nan gaba.
Oluremi Tinubu ta ce takarar Musulmi da Musulmi a yanzu zai kawo da sabon tsari a fagen siyasar Najeriya a 2023.
A cewarta, “Dangane takarar Musulmi da Musulmi, hakan zai haifar da tsarin da za a bi nan gaba.
“Wani lokaci nan gaba, za mu samu ’yan takara Kirista biyu, wannan kuwa abin mamaki ne da Allah Ya yi wa kasarmu,” in ji ta.
Ta yi wadannan kalaman ne a martaninta kan ce-ce-ku-cen da ake yi game da takarar shugabancin kasa na Musulmim da Musulmi a APC, Bola Tinubu da Kashim Shettima.
Ta bayyana hakan ne ranar Laraba a wajen gangamin siyasa na matan Jam’iyyar da aka shirya Legas.