Hukuma Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC), ta ba dukkan ’yan takarar Shugaban Kasa da na Gwamnoni daga jam’iyyu 18 wa’adin mako daya su gabatar mata da sunan Mataimakansu.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu ne ya sanar da hakan ranar Alhamis a Abuja, yayin wani taronsa da Kwamishinonin hukumar na Jihohi.
- Rukunin farko na maniyyata Aikin Hajji sun tashi zuwa Saudiyya
- ‘Tinubu ya yi wa Gwamnonin APC alkawarin Mataimakin Shugaban Kasa’
Hakan dai na nufin dan takarar PDP (Atiku Abubakar) da na APC (Bola Tinubu) da na NNPP, (Rabi’u Musa Kwankwaso) da sauran ’yan takarar dole su nada Mataimakansu nan da mako daya mai zuwa.
A cewar Shugaban na INEC, yayin da za a kammala dukkan zabukan fid-da gwani ranar Alhamis, za a fara nada Mataimakan ’yan takarar ne daga ranar Juma’a mai zuwa kuma a kammala cikin mako daya.
Farfesa Yakubu ya ce, “A cikin mako daya mai kamawa daga gobe [Juma’a], 10 ga watan Yunin 2022, ana bukatar dukkan jam’iyyu su gabatar sunan ’yan takararsu a zabukan matakin tarayya (Shugaban Kasa da ’yan majalisun tarayya), kafin nan da ranar Juma’a, 17 ga watan Yuni.
“Zabukan natakin Jihohi kuwa (Gwamnoni da ’yan majalisun Jihohi, za a dora sunayensu ne daga daya zuwa 15 ga watan Yuli, kamar yadda jadawalinmu da muka fitar na zabukan 2023 ya nuna,” inji Farfesa Yakubu.
Shugaban na INEC ya ce dukkan jam’iyyun za su dora sunayen ’yan takarar ne a shafin da hukumar ta tanada (ICNP) a gurbin kowacce mazaba.