Fadar Shugaban Kasa ce ta ce babu dan takarar da Shugaba Muhammadu Buhari zai bincika saboda sayen fom din neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC na Naira Miliyan 100.
Kakakin Shugaban, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan ne a shirin gidan talabijin na Channels ranar Alhamis.
- An kashe mutum 40 da Karamar Sallah a Taraba
- NUC ta ba sabbin jami’o’i masu zaman kansu 12 lasisin fara karatu
Yanzu haka dai akwai akalla ’yan takara 30 da suka sayi fom din, to sai dai Kakakin ya ce aikin hukumonin yaki da rashawa ne, da ’yan jaridu, da kungiyoyi masu zaman kansu binciko yadda aka samo kudin ba wai Shugaban Kasa ba.
Ya ce, “Tambayar a nan ita ce a ina suka samo wadannan kudaden? A ganina kowanne ya dace ya amsa tambayar nan, amma ’yan jarida da kungiyoyin farar hula ne ya kamata su yi ta,” inji shi.
Ya ce maganganun da ’yan Najeriya ke yi cewa Buharin ya binciki yadda suka samo kudin ma bai taso ba, don ba mafita ba ce a cewar Garba Shehun.
“Idan hukumar ICPC ko EFCC sun ce Babban Sakatare ina ka samo kudin fom? Shugaban kasa ba zai ce uffan ba”. In ji Garba Shehu.
Dangane da farashin fom din kuwa Garba Shehu ya ce kamata ya yi a yaba wa jam’iyar bisa kudin da ta yanke, domin a cewarsa ba ta bukatar kudin asusun kasa domin gudanar da yakin neman zaben.
“Jam’iyar ta kare wannan batun kuma dole a yaba wa shugabanta na kasa, saboda hakan na nufin ba a satar dukiyar al’umma ayi aikin jam’iya da su,” inji Garba Shehu.