Mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar APC, Rochas Okorocha, ya ce kaf cikin masu neman takarar babu wanda zai iya samun kuri’u daga Arewacin Najeriya kamar yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake yi a baya kamar shi.
Rochas, wanda tsohon Gwamnan Jihar Imo ne ya kuma ce farin jininsa a siyasance ya ma fi yawa a Arewa fiye da a kowane yanki.
- Ba za mu yadda a yi sulhu a fitar da dan takarar APC ba — Magoya bayan Tinubu
- ‘Rashin audugar al’ada na jefa mata cikin tsaka mai wuya’
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake tsokaci ranar Laraba, kan batutuwan da suka dabaibaye batun gudanar da zaben fid da gwani na kujerar Shugaban Kasa a APC.
Kiris dai ya rage tsohon Gwamnan na Imo bai kuskure tantance masu neman takarar da APC ke yi ba saboda yana hannun hukumar EFCC bisa wasu zarge-zarge guda 17 da take masa, wadanda suka jibanci karkatar da kudade lokacin mulkinsa.
Sai dai jim kadan bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya bayar da belinsa a ranar Talata, ya garzaya wajen da ake tantance masu neman takarar.
Da aka tambaye shi kan cancantar shi ta tsayawa takarar, Rochas ya ce, “Tambayar da ya kamata APC ta yi wa kanta a yanzu ita ce wanne dan takara ne zai iya samo mata yawan kuri’u a Arewacin Najeriya kamar yadda Buhari yake yi a baya?
“Duk wani abu koma-bayan haka son zuciya ne kawai. Saboda yanzu abin da kawai PDP take tutiya da shi, shi ne za ta samun tarin kuri’a daga Arewa. Wannan kuna gaskiya ne.
“A wannan karon kuma babu Buhari a cikin zaben. Kuma a matsayin shi na wanda ya mulki Najeriya tsawon shekara takwas, dole akwai matsaloli, dole ba za a sami irin kuri’un da ba, ka ga akwai kalubale ke nan. Saboda haka, ya zama wajibi a duba a ga wanne mutum ne zai iya samo wadannan kuri’un daga Arewa?
“Ina ganin ni ne wannan mutumin, saboda na fi farin jini a Arewa ma fiye da a kowane yanki,” inji shi.
A ranar 25 ga watan Mayu ce dai EFCC ta cafke Rochas Okorocha, wanda shi ne Sanata mai wakiltar Imo ta Yamma, a gidansa da ke Abuja.