✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Babbar hanyar yakin neman zabe ita ce gyara gadojin da suka karairaye – Sheikh Jingir

Ya kuma yi kira ga 'yan siyasa da su yi kamfen ba cin mutuncin juna

A yayin da da aka fara yakin neman zaben shekara ta 2023, a ranar Larabar nan, fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce babbar hanyar da yan siyasar za su bi wajen kamfen ita ce su gyara gadojin da suka karye a daminar bana.

Sheikh Jingir, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta kasa, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Jos.

Ya ce, “’Yan siyasar nan wadanda muke yi musu zaton suna da dukiya, da suke takara muna jan hankalinsu kan su hada kai da ’yan siyasar da suke kan mulki, don a gyara gadojin kasar nan da suka kakkarye a daminar bana.”

Malamin ya ce wannan ita ce babbar hanyar jan hankalin masu zabe a kasar nan, musamman idan aka dubi mawuyacin halin da al’umma, suka shiga sakamakon wadannan abubuwan.

Ya yi kira ga ’yan siyasar da kada su zama masu zagin juna a lokacin yakin neman zave.

Kazalika, malamin ya ce ja hankali a kan dibar matasa ana raba musu miyagun kwayoyi su karkashe junansu, a lokacin yakin neman zaben.

“Al’ummar Najeriya su guji kwadayi, kada su zabi mutane don an basu kudi ko don kabilanci. Mu kiyayi kwadayi mu kiyayi kabilanci, mu zabi shugabannin da suke da cancanta,” inji Sheikh Jingir.

Shehin malamin ya kuma ja hankalin masu wa’azi da sauran al’ummar kasar nan da su taru su yi addu’ar Allah ya ba kasar shugabanni masu tausayi.