Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar APC ya amince da nada wasu ’yan masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood a cikinsa.
Darakta-Janar na kwamitin kuma Gwamnan Jihar Filato, Simon Bako Lalong, ne ya amince da nadin.
- Muna bukatar karin kudade don yaki da barayi – Shugaban EFCC
- Wanda ya kashe Musulmi 51 a New Zealan ya daukaka kara kan hukuncin kotu
Sanarwar nadin kuma na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Kakakin Gwamnan, Makut Simon Macham, wacce aka fitar ranar Talata.
Sanarwar ta ce, nadin ya biyo bayan wani taro da dan takarar Shugaban Kasa a APC, Bola Ahmed Tinubu ya ya yi da ’yan masana’antar a Kano, inda suka tabbatar da suna tare da shi.
Bayan baje fasaharsu a gaban dan takarar, sai ya yi musu alkawarin samar musu gurbi a kwamitin yakin neman zaben don tallafa masa wajen cim ma burinsa na zama Shugaban Najeriya.
Sanarwar ta kuma ce Gwamna Simon Lalong, ya baukaci ’yan masana’antar da su tattaro masoyansu don a hadu a mara wa dan takarar baya, tare da kira gare su da su ba da himma wajen tallata shi yadda ya kamata.
Daga cikin ’yan tawagar Kannywood din akwai Abdul Moh’d Amart (Mai Kwashewa) a matsayin Darakta da Ismail Na’abba Afakallah a matsayin Mataimakin Darakta, sai Sani Mu’azu a matsayin Sakatare da dai sauransu.