✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2015: Sai Buhari?

Abin da zan fada yau ba wani sabon abu ba ne, na fada a baya, na kuma sha fada a duk lokacin da irin wannan…

Abin da zan fada yau ba wani sabon abu ba ne, na fada a baya, na kuma sha fada a duk lokacin da irin wannan dama ta samu, wato duk lokacin da Janar Buhari ya fito domin neman kujerar shugabancin kasar nan. Na taba bayyana shingayen da nake jin za su kasance a gabansa kafin ya kai gaci, a matsayin shawara domin a dubi tunanin a kawar da su in ana son a samu nasara.

Haka na sha tattauna matsalolin da za su iya addabar shugabancin Buhari in har ya ci zabe, wadanda za su iya kasancewa daga gare shi ko magoya bayansa.
Na sha yin kira ga masoyansa domin su fahimci abin da ke sa Buhari faduwa zabe a duk lokacin da ya fito takara. A nan ba ina nufin wa ke kada Buhari ba, ME ke kada shi, domin abubuwa ne masu yawa.
Yau ma abin da zan yi ke nan, in sake bibiyar abubuwan da suka faru a baya da ganin ko za mu tsinkayi wani sabon abu daga wannan takara da ake kai yanzu ta zaben 2015, kamar yadda na taba nunawa bayan zaben 2011.
Mu lura, koda aka fafata tsakanin Buhari da Jonathan a zaben shekarar 2011, wasu jama’ar kasar nan sun koka kan babban rashin da aka yi na ganin Janar Buhari bai ci zabe ba.Wasu sun koka kan cewa Najeriya ta shiga uku tunda Buhari ba zai mulke ta ba, bare ya kawo canjin da ake bukata.
Tun daga wancan lokaci yau kusan shekara hudu ke nan ba ta canza zane ba. Har yau inda muka fito nan muke ba mu motsa ba, bare a samu wani ci gaba. Me ya sa na ce haka? Kullum batun yawancin al’ummar Najeriya musamman na Arewa shi ne a matsa wa Buhari ya sake takara a shekarar 2015, domin a ganin irin masu wannan tunani, Buhari mutum ne mai gaskiya, kuma in ya ci zabe zai kawo canjin da ake bukata. Yanzu ga shi an sake matsa masa, ya sake jefa hula a cikin da’ira, amma batutuwan da muke ta fama kansu, har yanzu ba su canza ba, ba kuma alamar canzawa. Ni dai ban taba samun tababa ba game da gaskiyar Buhari, amma zan sake maida mu baya ne game da neman canji da al’ummar kasar nan ke bukata, musamman ganin Buhari ya sake fitowa takara.
Shin a wannan karo Buhari zai kai labari? Shin in an tsaida Buhari takara, zai iya cin zabe, kuma daga baya canji zai samu? Na yi wadannan tambayoyi ne domin da alama kamar talauci da kuncin rayuwa da yunwa da rashin sanin makamar siyasa da muke fama da su, wadanda kuma sun rufe mana idanu mun kasa fahimtar tuni gari ya waye za su iya zame mana kandagarki!
Mu koma ga wancan tambihi da na yi a 2011, na ce tambayar ita ce, ba yadda za a samu canji ke nan a kasar nan sai Buhari ya ci zabe? Ba wani mai iya kawo canji a kasar nan sai Buhari kawai? Ba wata jam’iyya da za ta iya kawo canji sai APC? Ba a iya sanya gwamnatin PDP ta kawo canjin tunda ita ke mulki a halin yanzu ko kuma in an kammala zaben 2015 ta sake hayewa karaga? Ba yadda za a yi a matsa wa Jonathan ya yi wa kasar nan abin da ya dace da ita in shi ne ya sake cin zabe a 2015, sai dai a ce mu jira sai nan da shekara ta 2019 ko ma fiye, mu sake zabar wani da zai kawo canji? Shin muna da lokacin sake jira don samun canji nan da shekarar 2019? Nan da wannan lokaci, ina Buhari? Ina APC? Ina PDP? Ina Talakawan Najeriya? Ina sauran gwamnonin da aka zaba da ba sa cikin Jam’iyyar PDP yanzu? Su ba su iya kawo canji, sai dai Buhari ko jam’iyyarsa? Wadannan na daga cikin batutuwan da ya kamata mu mayar da hankali kai.
Tambayar da nake faman yi wa kaina ita ce mun kuwa mayar da hankali a kan irin wadannan batutuwa tun bayan zaben 2011? Shin ba wata hanya ko mafita ko wani mai iya agaza wa kasar nan sai Buhari? Shin ba mu jin cewa irin wannan tunani shi ke sa al’amurranmu ba sa tagazawa, kullum sai faman gara jiya da yau?
Ni dai tun lokacin da aka yi wancan ‘zabe’ na 2011, har zuwa yau hankalina bai kwanta ba, kullum tunani nake yi na ganin ba mafita ga kasar nan dangane da shugabanci da ciyar da kasar nan gaba. Kullum na ji ana ta batun za a yi kokarin ganin an kawar da Jam’iyyar PDP ta kowace irin fuska, za a yi iya yi a kawar da Shugaba Jonathan daga mulki a zaben 2015, sai na kara fahimtar halin rashin mafita daga wannan tunani. Mu dauka cewa Jam’iyyar APC ta ki tsayar da Buhari don yakar Jam’iyyar PDP don a samu kawo canji daga shekarar 2015, shi ke nan canji ya yi hijira daga Najeriya? Mu dauka cewa ma an tsayar da Buharin a APC, amma aka gwabza, ba a samu nasarar kayar da Jonathan ko PDP ba a zaben 2015, shi ke nan al’ummar kasar sun ci gaba da shiga uku ke nan ba mafita daga halin da suke ciki? Ba wani abu da za a iya yi?
Za mu ci gaba