✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2015: Sai Buhari? (2)

Bari na sake nanata irin nawa tunanin wanda kuma nake ganin cewa yawancinmu shi ne ke tattare da mu. Me ya sa kullum tunanin al’ummar…

Bari na sake nanata irin nawa tunanin wanda kuma nake ganin cewa yawancinmu shi ne ke tattare da mu. Me ya sa kullum tunanin al’ummar kasar ya dogara kacokam kan Buhari a Jam’iyyar APC ko irin su Tinubu da Kwankwaso ko Fashola ko Ameachi? Ba wani ko wasu da za su shiga cikin wannan tafiya domin a samo mafita sai su kurum? Ba wasu masu iya motsawa domin kawo canjin da ake bukata a kasar sai ’yan Jam’iyyar APC ko Buhari ko Tinubu ko Kwankwaso ko Fashola? Ba wani abu ya sa ni yin irin wadannan tambayoyi ba sai yadda na ji wasu na ta sowa da murna wai an ce Buhari zai sake tsayawa takara a shekarar 2015, abin sai ya daure min kai, murnar me suke yi? Murnar ga mai fitar da talaka daga cikin kangi ya dawo ruwa, saboda haka daga shekarar 2015 in an ci zabe, an kama hanyar shiga aljanar duniya? Ke nan talauci da yunwa da fatara da kunci sun shiga uku, domin ga maganinsu nan zai yi takara, wato Buhari ko Jam’iyyar APC?

Ni dai wannan tunani ban yarda ya yi min katutu ba, eh, lallai ina bukatar canji, ina son na ga talaka na sakata yana walawa a kasar nan, idan kuma lallai Buhari ne musabbabi, zan so haka, idan kuma sai shekarar 2015 za a fara ganin alamun hakan idan an ci zabe, ba laifi, amma me ya sa muke zuba dukkan kwayayen da kazarmu ke yi a kwando guda? Me zai faru (ba addu’a nake yi ba) idan Buhari bai ci zabe ba, in an tsayar da shi a shekarar 2015, shi ke nan canji ya bar doron kasar Najeriya har abada?
Ba ma wannan kadai ba, ni gabana faduwa yake yi in na tuna ga Buhari can ya ci zabe a shekarar 2015, amma mu da muka zabe shi mun hana shi sakat! Mun sa shi gaba sai faman sukarsa muke yi, canjin da muke hankoro ya ki samuwa, ko mun hana shi samuwa. Ba wai, Buhari mutumin kwarai ne! Mutum ne mai son gaskiya da rikon amana! Mutum ne da ke da zuciyar taimaka wa talaka! Mutum ne mai son a yi abu bisa ka’ida da daidaito! Mutum ne da ba ya son handama da babakere! Amma ita tafiya irin ta shugabancin kasa, musamman a Najeriya, ba tafiya ce ta mutum daya ba. Tsarin dimokuradiya ne, akwai bangaren Shugaba da bangaren Majalisun kasa da na Shari’a, idan ba a samu Buhari ko irin Buhari ba a sauran wurare ba, na tabbata damun furar ba zai yi armashi ba! Idan ma an samu irin Buhari ko wasu masu tunani irin na Buhari a matsayin shugabannin Majalisun Tarayya da bangaren Shari’a, amma ba a samu irin Buharin a cikin Majalisun ba ko sashen Shari’ar ba, ni sai na ga tamkar za a yi ungulu da kan zabo ne! Ba ma wannan ba, idan an samu komai ya yi daidai daga ’yan kwallon Najeriya, Kyaftin Buhari na cikin fili da shi da su Okocha, ya samu goyon bayan irin su Messi ko Ronaldo ko Iniesta. Ga gola na kwarai irin su Casillas, shi ke nan komai ya yi daidai ke nan da ’yan wasan, shi ke nan sai cin kwallo ba kakkautawa?
Shin ba mu tsayawa mu nakalci sauran ’yan wasan da dole sai da su za a iya cin kwallo, idan kana da Messi a cikin ’yan wasanka, amma can baya ba ka da masu tsaron baya na kwarai, ina amfanin wannan tsari? Shin mu tambayi kanmu, ’yan wasan ne kadai ke kai ga nasarar wasa a filin kwallo? Ina ’yan kallo? Ina alkalan wasa da mataimakansa? Ina filin kwallon shi kansa, yaya yake? Ina kwallon da sauran abubuwa da za su sa a shura tamola lafiya, a kuma samu nasara kamar but da safa da sauransu? Ke nan matsalar Najeriya da halin shugabancin da ke addabarta ba wai kawai Buhari ne magani ko mafita ba, idan ma na ce ba mu bukatar Buhari a shekarar 2015, ina jin ban shara ta ba! Me ya sa? Lallai idan da Buhari a matsayin Shugaban kasa a Najeriya daga 2015 wasu abubuwa za su canza! Amma canji na kwarai ni a nawa tunani bai samuwa a kasar nan sai mun yi watsi da Buhari, mun kama akidojin Buhari! Idan yawancinmu mun dage kan akidar nan ta wawura da sata da cin hanci da almubazzaranci da kisan mummuke da nuna son kai da wariya da makamantan haka, ba inda kasar nan za ta je!
Idan har Buhari na can Aso Rock yana gudanar da lamurra yadda zai kawo canji, amma ministoci da gwamnoni da ’yan majalisa da ciyamomi da kansiloli sun manta da akidar Buhari, ba wani canji da za a samu! Ba fata nake yi ba, amma a auna tunanin da kyau a ga ko akwai abin bincina daga ciki! Lokaci ya yi da za mu auri Buhari da dukkan halayyarsa, tun yanzu ba wai sai shekarar 2015 ba! Allah Ya yi taimako!